Yadda Ake Gyaran Nono Ga Budurwa |
Hanyoyi Yadda Ake Gyaran Nono Ga Budurwa Har Da Mata Masu Shayarwa
Wannan wani hadi ne da akeyi don gyaran nono musamman ga budurwa, shi wannan hadi kuma kowace mace idan tana bukata za ta iya amfani dashi saboda tasirin da yake yi wajen gyara nono mace.
Yadda akeyi wannan hadin shine za a samu wannan abubuwan kamar haka;
- garin waken soya
- garin alkama
- garin zogale
- garin bawon lemun zaki
- kunfan Maliya da
- zuma
Yadda Ake Gyaran Nono Ga Budurwa
Idan kun samu wannan abubuwan guda 6 sai ki hada su guri daya, sannan sai ki rinka shafawa a kan nono ki, bayan kamar minti 30 ko sama da haka sai ki wanke. Sannan kuma ki rinka shan kunun alkama zaki sha mamaki domin zai taimaka miki wajen cikowar nono ki.
Yadda Za Ki Dawo Da Maratabar Nono
Don dawo da maratabar nono da girmansa da cikar sa.
Ga matar da take son ta dawo da martabar nononta ko girmansa yanda za ta yi shine za ta samu wanna abubuwan;
- ganyen sabara mai kyau
- 'ya'yan alkama
Sai ki rinka kunu dasu, ko kunun gyada, ko kunun alkama, ko kunun shinkafa, ko kunun gero, ko koko, duk dai wanda ya samu ko wanda ranki ke so, sai ki dafashi da wannan hadin mai albarka.