Yadda Ake Gane Bayyanar Cuta a Jikin Mutum |
Yadda Ake Gane Bayyanar Cuta a Jikin Mutum
Ita dai cuta tana bayyana ne a jikin mutum ta hanyoyi ukku wadanda a turance sune Sign, Symptom da Syndrome.
Sign:-alama ce ta cuta wadda take, wani Wanda ba Mara lafiyar ba zai iya gani kuma ya ga cewa akwai alamun rashin lafiya. Misalan sign sune kumburi, kurarraji, tari da sauran su.
Symptom:- alama ce wadda shi mara lafiya ne kawai zai iya ji kuma ya fada. Misalan symptom sune ciwon kirji, kassala, ciwon gabbai da dai sauran su.
Syndrome kuma, gamayya ce ta signs da symptoms masu dangantaka da juna wurin bayyana kasantuwar wata cuta a jiki. Misali cutar Kanjamau syndrome ce saboda signs da symptoms ne a hade suke bayyana kasantuwarta.
Yadda Ake Gane Bayyanar Cuta a Jikin Mutum
Abubuwan da suke da tasiri akan yiwuwar cuta ta kama mutum sun hada da:-
-Yanayin karfin garkuwar jikin mutum (Immunity of the host)
-Adadin (yawan) kwayoyin cutar da suka shiga jiki (dose of infectious agent)
-Karfin kwayar cuta wajen iya sa cutar (pathogenicity)
-Karfin kwayar cutar wajen iya samar da guba (toxigenicity)
-Karfin kwayar cuta wajen iya hayyayyafa ta mamaye sassan jiki (invasiveness) Da dai sauran su.
Saboda banbance banbance da ke akwai tsakanin mutum da mutum, za a ga cewa cuta iri daya na iya kama mutane daban daban amma tasirin ta ya sha banban a tsakanin mutanen. Wani ya sha wuya sosai har ta kai ya rasa ran sa. Wani kuma ta dan taba shi ya dan sha wuya ya mike.
To amma akan samu mutane wadanda ga su suna da cutar amma kuma ta zama bata bayyana ko daya ba, daga cikin alamomin kasantuwar ta. Ta yiwu alamomin su bayyana daga baya. Ta yiwu kuma kwata kwata ma alamomin ba za su bayyana ba duk da cewa akwai cutar. To wannan irin kamuwa wadda babu alama, ita ake kira Asymptomatic. Watau ga dai cutar amma kuma ba za ta nuna alamar kasantuwar ta ba.
Ya na da kyau idan har mutum yana da asymptomatic infection, watau cuta wadda ba ta nuna alama ba sai dai kawai awo ya nuna, indai cutar irin wadda ake dauka ce daga mutum zuwa mutum, to mai cutar ya kamata ya dauki matakan kare iyalan sa, da yan uwansa da masoyan sa da sauran alumma. Dalili kuwa shine; idan shi a jikin sa cutar ba ta nuna alama (asymptomatic) to ta yiwu idan wani nashi ya dauka, shi ta bayyana kuma ta yi tasiri mai yawa a jikin sa. Ko dai ya sha wuya ya tashi ko kuma ya rasa ran sa. Allah Ya kiyaye.