kalaman soyayya na kwanciya bacci |
Dole na zamto mai faranta miki, dole inyi yaki, dole na jajirce, dole nayi adawa da duk wanda yakeso ya rabani dake.
Kalaman soyayya na kwanciya bacci na daga cikin abinda ke kara soyayya tai karfi a tsakanin masoya. Domin kuwa Kalaman kwanciya bacci sune masoyi ke kwanciya dashi a ransa idan aka furta masa su. Sai dai ba kasafai masoya ke yin amfani da kalaman soyayya na kwanciya bacci tsakanin su ba hakan yasa muka tattaro muku su.
Kalaman Soyayya Na Kwanciya Bacci
Ga jerin kalaman soyayya na kwanciya bacci da masoya za su furtawa junansu;
BACCINA
Ni na kasance cikin masu kasa bacci a yayin da dare ya tsala bani da komai sai tinaninki har wani gari kan wayewa ban'iya rintsawa nasan wannan yana faruwane saboda tsantsar soyayyar da nake miki
ADAWAR SO
Dole na zamto mai faranta miki, dole inyi yaki, dole na jajirce, dole nayi adawa da duk wanda yakeso ya rabani dake.
SAKON SO
Kin san cewa a tin lokacin da idaniyata suka sauka akan kyakykyawar fuskarki zuciyata ta gaza kasa tinaninki, tabbas sanki ya shiga zuciyata.
KYAUTAR SO
Masoya kanyi kyauta musamman ga junansu kamar; zoben so, furan so, akalar so, frames mai dauke da kalaman so
SO-SO
Hasken farin wata kan haskake sararin samaniya taurari ma'abota haske sukan kasance cikin dare amma sunfi kyau idan da wata a tare dasu hasken fuskarki yana karamin farin ciki da bazai misaltuba saboda girman son da nake miki cikin zuciyata.
Wannan sune wasu daga cikin kalaman soyayya na kwanciya bacci da ya dace masoya su dinga yiwa junansu. Da fatan kalaman soyayya da kuka Karanta kun ji dadin su.