kalaman soyayya A farkon haduwa |
Kalaman soyayya na farkon haduwa tsakanin masoya sune ke tasiri wajen tabbatar da soyayya ga masoya
Akwai wasu kalaman soyayya masu rasta zukatan masoya da ya kamata masoya su sani musamman a haduwar farko. Domin furta Kalaman soyayya ga masoyi ko masoyiya a farkon haduwa shine suke tasiri har a samu soyyaya ta dore.
Duk budurwa ko saurayi idan ya iya furta kalaman soyayya ga masoyiya ko masoyi babu shakka za'a samu soyayya mai dadi da inganci. Don kuwa furta kalaman soyayya suna da tasiri sosai wajen cigaban soyayya.
Yadda Za Ka Furta Kalaman Soyayya A Farkon Haduwa Da Masoyiyarka
kallon farko da nayi miki na fahimci cewa kina da baiwar da duk wani da namiji zaiji yana son ki. baya ga haka ke kyakkyawace, na dade ina neman hanyar da zan furta miki kalaman soyayya ta, sai dai zuciyata tana jiye min wani abu, da zaki amince da soyayya ta da nayi farin ciki. Domin na dade ina fatan naga cewa mun kasance masoyan juna ni da ke, hakika babu wata makusa a gareki domin kinada kyawun da kowa zaiso yayi rayuwa dake.
Idan har zaka iya furta irin wadannan kalaman soyayya ga masoyiyarka tabbas za ka sace zuciyarta cikin kwanciyar hankali ba tare da bata lokaci ba. Da fatan masoya an koyi darasi kan yadda ake furta kalaman soyayya a haduwar farko.