yadda ake dadewa a kwanciyar aure:

Maryam Ceter: yadda ake dadewa a kwanciyar aure
yadda ake dadewa a kwanciyar aure

yadda ake dadewa a kwanciyar aure don ma'aurata 


Kusan duk mutum daya a cikin uku suna fama da saurin yin inzali ko kuma saurin biyan buƙata a yayin kwanciyar aure a lokacin da matar ko mijin bai so ba. Duk da cewa akwai magunguna da za’a iya amfani dasu wajen magance wannan matsalar, amma akwai hanyoyi da idan mutum yabi zai sami sakamako mai kyau.


Zamu tattauna akan wadannan abubuwan

- Ka gano tsakar PC.

- Ka tsaya daga saduwa.

- Kuyi wasa kafin saduwa.

- Chanza yanayi.

- Kayi a hankali.

- Ka gwada hanyar 7 da 9.

- ka gwada hanyar jinkirtawa da kuma matsawa.

- Karfafawa kanka gwiwa.

- Ku tattauna da matarka.

- Ka nemi shwarar likita.


Hanya ta daya: a shiryawa saduwar

1. Ka gano tsakar azzakari. Akwai wata tsoka dake tsakanin mafitsararka da kuma duburarka. Idan kana san nemo wannan tsokar azzakari, zaka shiga bandaki ne domin yin fitsari, kana cikin yin fitsarin sai kayi kokarin tsayar dashi, wannan tsokar da kayi amfani da ita wajen tsayar da fisarin, itace tsokar gaban mace da ake magana.


Ka bawa kanka lokacin domin da ɗame wannan tsokar ta hanyar mostata ta hanyar ɗame ta. A kalla yana da kyau ka mosta ta sau 15 a rana domin ya taimaka maka da dare. Hakan zai taimaka maka wajen kiyaye lokacin da kake son yin inzali a yayin kwanciyar aure.


2. Ka tsaya daga saduwa. Akwai mutanen da suke bukatar su dan daina saduwa na wani lokaci. Kayi magana da matarka sannan kuma ku tattauna da likitanka akan matsalar ka. Amma bana nufin ka daina kula kwanciyar aure da matarka ba, zaku dinga wasa na soyayya amma kuma banda saduwa. Hakan zai na koya maka yadda zaku zauna cikin farin ciki ta hanyar ɗauke maka cewa dole sai kun sadu.


ka kwantar da hankalinka ko ka rage sauri a yayin kwanciyar aure

3. Kuyi wasa kafin saduwa. kwanciyar aure wani irin abune mai ban mamaki. Kowa ya sani cewa namiji yana yin duk wani abu domin kar yayi inzali da wuri, ita kuma macen tana yi duk wani abu domin tayi inzali da wuri.


Saboda haka, ku dinga wasanni kafin saduwa, kamar sumbata, amfani da baki, da sauran abubuwan da baza’a rasa ba. Hakan zai taimaka wajen bawa matar gamsuwa.


4. Canza yanayi. Yana da kyau ku dinga chanza yanayin Kwanciyar aure lokaci bayan lokaci domin hakan zai nuna maka wasu abubuwa da baka sani ba a baya na jin dadi.


Wata hanyar canja yanayin kwanciya shine idan kuna tsakiyar saduwa. Da zarar kaji zakayi inzali, kayi sauri wejen chanza yanayin kwanciyar.


Daya daga cikin yanayin da zai taimaka anan shine idan macen tana samanka.

5. Kayi a hankali. Ka dinga bawa kanka lokaci tsakanin shiga da fita da kake yi misali kamar sakanni uku tsakani. Kar ka dinga sauri ko gudu domin hakan zai sa kayi inzali da wuri.


- Duk lokacin da kaji zakayi inzali, sai ka rike a ciki har ka samu nutsuwa sannan ka ci gaba.

- Wata hanyar daina sauri itace ka dinga amfani da sauran bangarorin jiki ta hanyar tabawa ko sumbata.


4. Ka gwada hanyar 7 da 9. Akwai abinda masana suke kira da 7 da 9, yadda akeyi shine a yayin kwanciyar aure ka shiga ka fito da sauri sau 7 sannan kuma ka shiga ka fito a hankali sau 9. ka ci gaba da yin hakan har ku gama a ranar.


5. ka gwada hanyar jinkirtawa da kuma matsawa. Wannan hanyar tana bukatar matarka ta taimaka maka wajen matse gaban naka a lokacin da kaji alamar zaka yi inzali musamman kusa da kan. A rike shi a wasu ‘yan sakanni har sai kaji ka daina jin cewa zakayi inzalin, sai ka jira sakanni kamar talatin sannan a koma yin wasan soyayya kuma.


samun kwarin gwiwa.

6. Karfafawa kanka gwiwa a yayin kwanciyar aure. Zaka iya bawa kanka kwarin gwiwar cewa zaka iya yin abinda kake so. Da zarar ka fara jin cewa ka karaya, sai ka daina tinanin karayar ka koma tinanin jin dadin da kakeyi da kuma cewa tabbas zaka iya dadewar da kake so.


7. Ku tattauna da matarka. Yana da kyau ku zauna kai da matarka domin kuwa tana da hakki na ka dinga gamsar da ita wajen Kwanciyar aure. Idan da baka saurin inzali sai yanzu ka fara, zata iya yiwuwa matsalolin da suke faruwa ne a tsakaninku wanda zaku tattuna domin magance ta.

- tattaunawa tare da ita zai sa ta baka shawarwari da take tinanin zasu taimak muku wajen dadewa a yayin da kuke Kwanciyar aure. Misali, canja yanayin kwanciya, chanza yadda kuke wasannin soyayya da sauransu.


8. Ka nemi shawarar likita. Zata iya yiwuwa kana da wata cuta ne a jikinka wanda take sawa kake saurin yin inzali. Saboda haka, likita zai duba ka sannan ya fada maka abubuwan da ya gano a kanka.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post