Yadda Ake Bayyana Kalmomin So Ga Masoyiya |
Kalmomin So: Sarauniyata rabuwa dake akwai damuwa haduwa dake akwai farantuwa, wanzuwar kice kullum ke karuwa shiyasa nabaki amanar zuciyata
Yawaita yunkurin yiwuwar yayata manufar kaunarki a zuciyata bakina ya dauki al'kawari shiyasa zakiji bana gajiya da yi miki kalaman so da kauna, haka taswiyar kyakykywar hallitarki ce madubin da nake kallo kullm a idanun zuciyata, hakanne yasa na haddace asalin kyawun Kyakykywan kamanninki sala-sala.
Sarauniyata rabuwa dake akwai damuwa haduwa dake akwai farantuwa, wanzuwar kice kullum ke karuwa shiyasa nabaki amanar zuciyata. A cikin zukatan da sukai nisa a tafiyar soyayyarki haka zuciyata ce da farko a cikin su, domin zuciyata ta nutse a kogin kaunarki masoyiyata
Farin ciki baya taba samuwa sai da kwanciyar hankali, sai gashi kuma ina samun walwala da farinciki silar kyakykyawar kulawar da kike bani a koda yaushe sahibata, samun kusancin zuciyata da taki tamkar wata wadatacciyar inuwar farinciki da shauki ce takemin inuwa akullum.
Nice words
ReplyDelete