Yadda Ake Amfani da Aloe Vera Wajen Gyaran Fata

Yadda Amfanin Yin Jima'i Akai-Akai Ga MACE MAI Ciki Ke Ƙara Musu Lafiyar Jiki Da Jaririnta
Yadda Ake Amfani da Aloe Vera Wajen Gyaran Fata


Yadda Ake Yin Amfani da Aloe Vera Wajen Gyaran Fata

Mata da dama musamman a lokacin sanyi na sha'awar ganin fatarsu ta yi sumul babu ƙuraje ko kaɗan. Wannan ganyen yana ɗauke ne da sinadarai da dama waɗanda sukan iya daɗa tsawon gashin mace, sanya fuska sheƙi, gyaran jiki da dai sauransu. Saboda haka ne a yau na kawo muku hanyoyin da za'a bi domin amfani da ganyen wajen gyaran fata da kuma gashin kai.


Inaso masu karatu su gane cewa a duk rubutun da nake yi, idan na lissafo ababen haɗin kwalliya, guda ɗaya daga ciki nake so a riƙa yin amfani dashi, domin yawan sanya wa fuska ababe da dama na haifar da fesowar ƙuraje.


Abubuwa Da Aloe Vera Keyi Wajen Gyaran Fata

1. Koɗewar fuska: yawan aiki ko shiga rana na sanya fuska ta yi baƙi ko kuma launinta ya zama biyu. A sami ganyen ‘aloe bera’ sannan a matse ruwan sai a matsa ruwan lemon tsami sannan a kwaɓa a riƙa shafawa a fuska domin gyaran irin wannan fatar.


2. Yanƙwashewar fata: wannan ganye na rage shekaru daga fuskar mutum. A matso ruwan sa sannan a haɗa da ruwar ‘rose’ sai a riƙa shafawa a fuska a bari na tsawon minti goma zuwa goma sha biyar kafin a wanke a kullum.


3. Domin fuska mai yawan gumi/maiko: a sami ganyen sai a dan kankare bayansa sannan a ɗora a tukunya da ruwa har sai ya yi laushi sannan a sauƙe a zuba zuma bayan ya huce sannan a shafa a fuska na tsawon minti 20 a kullum kafin a shiga wanka.


4. Domin gautsin fata: a markaɗa dabino da gurji sannan a matsa ruwan ganyen ‘aloe vera’ da ruwan lemun tsami sannan a shafa a fuska da jiki na tsawon minti talatin kafin a wanke.


5. Gyaran gashi: a matse ruwan ‘aloe bera’ sannan a haɗa da man zaitun a kwaɓa su sosai sannan a riƙa shafawa a fatar kai da kuma saman gashin a duk lokacin da aka yi niyyar wanke gashin kai kafin a wanke . Yin hakan na sanya baƙin gashi da kuma daɗa wa gashin tsawo da ƙarfi.


Waɗannan sune yadda ake yin amfani da ganyen aloe vera domin gyaran fata, da fatan kun amafana daga abubuwan da kuka karanta.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post