Tarihin Mufida Adnan Moofy Algaita - Android Pols

Tarihin Mufida Adnan Moofy - Android Pols
Mufida Moofy Algaita Dubstudio


Wannan bayanin Zaitaimaka Muku Wajan Sani Wacece Moofy, Mufida Adnan (Moofy) mawaƙiya, mai fassara Finafinan India Zuwa Hausa 


An haifi Mufida Adnan da akafi sani da Moofy a Shekarar alib1994, a cikin Birnin Kano. Moofy ta shahara a fanin waka da kuma fassara Film din India zuwa Hausa tare da Kamfanin Fassara na Algaita. 


Rayuwar Moofy 

Tauraruwa Moofy tayi karatunta na Firamari da sakandare a birnin Kano. Ba ta tsaya a nan ba moofy ta wuce karatun Digiri a Asibitin Mallam Aminu Kano inda take karatunta a fanin Lafiya.


Rayuwar Moofy A Fagen Waƙa Da Fim 

Haka zalika Moofy ta fara waƙa tun a shekarar 2011 a ƙarƙashin kamfanin ajiya na Algaita wato (Algaita records), bata tsaya a iya nan ba kasancewar daukakar Kamfanin nasu na Algaita sai tauraruwa Moofy ta shiga fassarar fina finan India zuwa Hausa a ƙarƙashin Kamfanin Fassara na Algaita wato (Algaita Dubstudio) a shekarar 2012.

Mufida Moofy Algaita Dubstudio
Mufida Moofy Algaita Dubstudio


Waƙoƙin Da Tauraruwa Moofy Tayi Tare Da Fassarar Finafinai Ta 

Moofy tayi waƙoƙi guda goma shabiyar (15) ƙarƙashin Kamfanin ajiya na Algaita wato (Algaita Record), haka zalika ta fassara Fina Finan India zuwa Hausa sama da guda Dari (100)

Cikin gwagwarmayar da tai cikin waƙoƙinta Moofy ta shaidawa Al'ummar Hausa cewa waƙar da tafi burgeta ita ce "My Fantasy" da kuma "ƙaunar ka*. Haka kuma ta shaida mana cewa waƙar da tafi bata wahala wajen yinta itace "Masuburbudar Chasu* domin tace waƙar ba irin salon waƙoƙin da ta saba yi bane. 

Mufida Moofy Algaita Dubstudio
Mufida Moofy Algaita Dubstudio


Lambobin Yabo Da Tauraruwa Moofy Ta Samu

Moofy ta samu lambobin yabo da na girmamawa da dama daga ƙungiyoyi da kuma Makarantu, daga ciki sun hadar da:

A Shekrar 2015 Moofy ta samu nasarar zama Mace ta farko a Arewa ta R&B, daga AMMA wato (Arewa Music and Movie Award).

Sai wata kyautar girmamawa daga Daliban FCE Kano.

Haka zalika a shekarar 2019 Moofy ta samu Lambar girmamawa daga ƙungiyar Taurarin Arewa, inda suka bata Best Female Artist. Da kuma sauran kungiyoyi da dama.


Ko Moofy Tayi Aure?

Haka zalika a tattaunawar da akai a ranar Alhamis 19 ga watan 6 2020, Moofy ta shaidawa Al'ummar Hausa cewa bata da Aure, Kuma kofa na bude ga duk wani namiji me tsoron Allah ,kyau,Tsafta da kuma son kamshi (Turare).


Mufida Moofy Algaita Dubstudio
Mufida Moofy Algaita Dubstudio

Mufida Moofy Algaita Dubstudio


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post