Sheikh Abdallah Gadon Kaya |
Taƙaitaccen Tarihin Sheikh Abdallah Gadon Kaya
Malam haifaffen garin Gombe ne (Kumo), Mahaifinsa kuma dan Giade ne (Bauchi) Shi ne farkon wanda ya kai Izala garin Giade. Daga baya karatu ya zaunar da Malam a Kano.
Matakin Karatun Sheikh Abdallah Gadon Kaya
Malam yayi karatu a Makarantar Legal ta Kano kafin tafiyar shi Madina.
Hakanan, Malam yayi karatu a wurin Malamai da dama, ya kuma bi zaurukan Malamai ya dauki ilimi. Daga cikin Malaman shi akwai;
– Sheikh Dr. Ahmad Ibrahim Bamba (Rahimahulla).
– Sheikh Abdulwahab Abdallah.
– Sheikh Ja’afar Mahmud Adam (Rahimahullah)
– Sheikh Dr. Muhammad Sani R/Lemo.
– Sheikh Dr. Bashir Aliyu Umar.
– Sheikh Dr. Muhammad Sani B/Kudu da sauran su.
Malam mahaddacin Alkur’ani ne, wanda Allah ya ba wa daddaɗan sautin karatun shi.
Malam yaje Madina yayi karatu a Kulliyatul Hadis, kamar yadda ya bibiyi wasu daga cikin majalisan Malaman wannan gari ya kwankwadi ilimi daga gare su.
Bayan dawowar Sheikh Abdallah Gadon Kaya daga Madina, ya dora Masters a Jami’ar Bayero ta Kano.
Sheikh Abdallah Gadon Kaya yaje kasar Sudan inda ya yi PhD ɗin shi a can.
Malam mutum ne me son ilimi da daliban ilimi, da kokarin karantar da shi. Kamar yadda Allah ya hore masa lafiyar fita yaɗa da’awa a sassan wannan ƙasa da ma maƙotan ƙasashe.
Malam mutum ne, me kyawawan ɗabi’u, wanda duk wanda ya zauna da shi zai fahimci haka. Ta yadda yake jan ɗalibansa a jiki sosai, da shiga cikin lamuran su.
Abinda Sheikh Abdallah Gadon Kaya Yake Yi A Halin Yanzu
Malam Limami ne a Masallacin Usman Bn Affan Gadan Kaya.
Kasancewar Malam karantarwa ya sa a gaba, hakan ta sa ya karantar da litattafai da dama a fannoni daban-daban, daga cikinsu akwai;
1. Umdatul Ahkam
2. Bulugul Maram
3. Riyadus Salihin
4. Sunut Tirmizi
5. Iziyya
6. Risala
7. Addurratul Bahiyya
8. Waraqat
9. Alwadhih fi Usulul Fiqh
10. Alqawa’idul Fiqhiyya
11. Usulus salasa
12. Alkawa’idul Arba’a
13. Kitabut Tauhid
14. Usulus Sunna na Ahmad
15. Kashfusshubhat
16. Aqidutud Dahawiyya
17. Aqidutul Wasidiyya
18. Juz’ul Kira’a Khalfal Imam
19. Alfiyatus Suyudi ta hadisi.
20. Alba’isul Hasis
21. Sharhus sunna na Bar
Wannan shine kaɗan daga cikin tarihin fitaccen malamin addini Sheikh Abdallah Gadon Kaya. Muna fatan Allah ya ja kwanan malam ya ƙara masa lafiya.
Daga Aliyu Shuaibu Aliyu