Sirrin Yadda Ake Sace Zuciyar Budurwa A Soyayya

Sirrin Yadda Ake Sace Zuciyar Budurwa A Soyayya
Yadda Ake Sace Zuciyar Budurwa A Soyayya


Sirrin Yadda Ake Sace Zuciyar Budurwa A Soyayya A Ranar Haɗuwar Farko


Duk irin girman kai da jan-aji da budurwa ke dashi akwai abubuwan da idan kana yi mata su a matsayin soyayya za ta saurare ka sosai kuma ta nuna maka soyayya. 


Sanin kowa ne jindaɗin rayuwa sai mutum ya sami irin macen da yake so sannan zai gane a daɗi yake ko a wahala.


Ta yaya zaka shawo kan macen da kake so ka rayu da ita Cikin soyayya?

To dakata kaji yadda ake shawo kan mace a soyayya.


Ita dai mace da kake gani, daga'yar shekara 1 zuwa 100, ma'aunin tunaninsu ɗaya ne. Harshen ka da ƙwaƙwalwarka, makamai ne masu ƙarfin da har yau mace bata mallaki garkuwar kare hare-harensu ba.


Idan kana so ka sace zuciyar budurwa da kalamai irin na soyayya, waɗanda za su ratsa ta duk jikinta su samu tabbataccen wajen zama a zuciyarta, ya zamana ba mai faɗa mata taji idan bakai ba, koda kuwa iyayenta ne domin irin kamuwa da tai a soyayyar ka.


Kalmomi ne kawai guda bakwai 4 zaka kiyaye wajen sace zuciyar budurwa ko matar ka a soyayya. Domin da su ne mace take jin lallai ta samu masoyi a soyayya, matuƙar idan taji su cikin bayanan ka da kake yi mata.


Budurwa tana so taji waɗannan kalamai ta bakin duk namijin da ya tsaya a gabanta domin neman soyayyar ta. Kuma da yawa daga matan basa gane ya akai ka iya sace mata tunani da zuciya.


Kada kayi ƙasa a gwiwa, daka ga budurwa kana neman soyayyar ta, kai tsaye ka tunkare ta ba tare da jin wata fargaba ba. Kana zuwa, dama fuskarka a sake take kamar kaga na gida.


Kalma ta farko da zaka furta budurwa idan ka tsaya da ita ta saurare ka komai uzurinta ita ce "Assalamu Alaikum," Idan ka furtawa budurwa wannan kalma duk irin uzurin ta sai ta baka amsa. Daga nan kuma sai ka ɗaura da abubuwan da za ka furta mata.


TSARI: Duk wata budurwa tana son ta ga namiji mai tsarin furta magana. Abin da nake nufi da haka shi ne, namiji ya kasance yana da tsarin iya magana mai ratsa jiki wanda dole a saurare shi.


KYAU DA KWALLIYA: Wasu ƴan matan abinda ke ɗaukar hankalinsu shine kwalliya namiji a lokacin da yai musu, mata suna son namiji mai kwalliya, duk irin yadda mace takai da girman kai idan taga wanda ya tsayar da ita ya yi kwalliya tana tsayawa ta saurare shi.


KALAMAI: Yana da kyau namiji ya zama ya iya kalaman da za su janyo hankalin duk wata budurwa, rashin iya kalami kan janyo mace taƙi sauraren saurayi a karon farko. Maimakon haka sai ka zama tamkar ɗan bora a soyayya. Dole ne ka kasance ka iya kalaman da zaka birge budurwa har ta ji ta kamu da da soyayya ka.


BARKWANCI: Ka ka kasance mai raha da barkwanci ga budurwar da ka tsayar da ita a karon farko. Hakan zai ƙara mata ƙarfin gwuiwa sauraron ka. Kana mai ambaton kalamai da za su sakata murmushi da da dariya. Ka yi mata zance cikin murmushi da shauƙi irin na soyayya Wanda zai sa dole hirarku ta kasance mai amfani ba ka yi ta zuba ba, har sai ka gundure ta. Yawan magana ba shi da tasiri a soyayya muddin ba magana ne masu ɗauke hankali da san ji ko rashin gundura ba.


Waɗannan sune yadda ake sace zuciyar budurwa a haɗuwar farko, wanda duk irin girman kai da jiji da kai irin na budurwa idan ka yi mata waɗannan kalamai za ta saurare ka har ta karɓi soyayyar ka.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post