Sirrin Kwanciyar Aure Don Ma'aurata

Sirrin Kwanciyar Aure Don Ma'aurata


Idan Ma'aurata Sun San Sirrin kwanciyar Aure, Za Su Samu Ƙarin Kaunar Juna Da Zaman Lafiya A Zamantakewar Aurensu 


Assalamu'alaikum yan uwana matan aure yau Insha Allah za mu yi bayani ne kan sirrin kwanciyar aure domin amfanin ma'aurata. Domin ana samun masu aure da yawa da suke cikin duhun kai akan wannan bangaren. 


Wasu basayi wasu kuwa suna yi ne kawai batare da sanin ilimin sirrin kwanciyar aure ba, kuma ba tare da sun san sirrin dake cikin shi ba. Abinda muke so ma'aurata ku fahimta shine duk maganin da za ku yi amfani amfani dashi Indai har baku san sirrin kwanciyar aure ba yana da wuya ku gamsar da junanku, kuna wahala ne kawai, kuma ba za ku taɓa gamsar da juna yadda ya kamata ba.


Saboda ta hanyar sanin kwanciyar aure ne za ku gamsar da junanku, shi yaji duniya babu kamar ki, kema kiji babu kamarsa. Mata ku sani cewa mijinki kowaye shi kowane irin hali gareshi wlh a tafın hannunki yake, sai dai idan ke bakisan sirrin kwanciyar aure ba, babu wani batun boka ko malan, kawai ku san sirrin kwanciyar aure.


Mafı yawan matan aure sune suke koyawa mazajensu neman matan banza duk don rashin iya kwanciyar aure, idan kika yi tunani menene matan banzan suka fiki, diri ko kyau koke farjin ne baki dashi. Abinda zai baku mamaki shine matan hausawa babu abinda suka iya sai mugun kishi, ai 'yar uwa idan kina da kishi karki nuna sai a yayin kwanciyar aure


Idan mace ta iya kwanciyar aure za ta sace ruhin mijinta, ta yadda zai kasance baya hangen kowace mace sai ke, zai ji cewa kece ruhin zuciyar shi, zai dinga ganin duk cikin mata ke daban ce. Abin mamaki shine yadda za ka samu wasu matan basa mayar da hankali kan yadda za su samu kaunar mijinsu ta hanyar kwanciyar aure sai dai su yi ta yin asiri.


Sirrin kwanciyar Aure

Idan ma'aurata suka san sirrin kwanciyar aure ba za ka taɓa jin wata matsala tsakanin su ba. Idan miji ya iya sarrafa matarsa, idan ya iya yi mata wasannin dake motsa sha'awar ta da yadda zai yi mata abubuwan da zai gamsar da ita kullum ƙaunar sa ƙaruwa yake a zuciyarta. Sanin abubuwan da matarka take so a yayin wasannin motsa sha'awa da lokacin saduwa da ita yanada da matuƙar tasiri a ɗorewar zamantakewar aure.


Kuma mata idan kuka cire kunya da girman kai kuka fahimci irin wasanni sha'awa dake sa namiji jindaɗi da gamsuwa ai kin gama mallake shi. Ki tabbatar a yayin kwanciyar aure kin yi abubuwan da zai gamsar dashi sosai, kuma ku kasance cikin tsaftar gyaran jiki da wajen kwanciyar aure.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post