Sirrin Gyaran Nono: Yadda Zaki Tsufa Da Nonon Ki A Tsaye

Sirrin Gyaran Nono: Yadda Zaki Tsufa Da Nonon Ki A Tsaye

Sirrin Gyaran Nono: Yadda Zaki Tsufa Da Nonon Ki A Tsaye


Sirrin Gyaran Nono: Yadda Zaki Tsufa Da Nonon Ki A Tsaye 


Nonuwa, ko nono ko kuma mama kamar yadda wasu suke cewa, wasu kulatai ne guda biyu da suke tsira daga kirjin mace da zaran ta soma balaga, ma'ana fitowarsa yana cikin alamomin balaga na mata. Ku kalli wannan VIDEO don don jin bayani 


Bayaga halitta ne da Mahalicci yayi domin alamta balaga ga mace, har ila yau nono yana cikin alamomin dake bambamta jinsi na mace dana namiji, domin duk macen da ta haura munzalin balaga kuma akaga cewa babu wani tsiro na nono daga kirjinta ya zama matsala kamar yadda za ku ji a wannan VIDEO.


Haka nan namijin da duk aka ganshi da nonuwa a kirjinsa tamkar mace, to ansan da matsala. Haka kuma nono dama yafi na hagu tsayi na kowace mace. Haka nan kuma Allah Ya halicci nono a jikinki mace ne domin ta samu wajen adana abincin jinjirin da zata haifa, ganin ruwan nonuwan mace shine abincin da jinjiri yake iya amfani dashi a matsayin abinci na wani lokaci mai tsawo kafin ya soma cin wani abinci mai nauyi.


Har ila yau shine abu na farko dake bayyanar da kyau ga 'ya mace da zaran sun soma fita daga kirjinta kuma suka kai munzalin girmansu. Don haka nema masana kwalliya da kyele-kyele suke cewa macen da take da cikakken nonuwa tafi kyau idan tayi kwalliya fiye da wacce bata da cikan kirji. Anan manufa shine baya ga abubuwan da muka ambata a baya, nonuwan mace suna kara kawata mata kyaunta fiye da mara shi.


A bangaren jima'i kuma, nonuwan mace yana dauke da kusan kashi 35 wajen samar da dadin dake cikinsa, domin idan kika kasa mata kashi 100, 70 daga cikinsu sha'awarsu na saurin motsawa ne da zaran anyi musu wasa da nonuwansu. Tabbasa da wadannan dalilan kadai ba zamu ga cewa, nonuwa a jikin mace ba karamin hikima da baiwa Allah Yayi a halittansu ba, don haka ya zama dole ga mata su bi duk wata hanyar da zasu bi na halak domin ganin cewa suna kula dasu.


Sai dai kuma shi kansa nono a jikin mace kowacce da irin yadda Allah yayi mata nata halittan ku saurari wannan VIDEO, wasu matan har su tsufa su koma ga Mahaliccinsu basu saka rigan nono saboda kankantar nonuwansu, wasu kuma rigan nonon ma baya isarsu saboda girmansa. Wasu nonuwan madaidaita ne marasa faduwa komin tsufan mace, wata ko da zaran ta soma haihuwa sun zama kamar silifa. Gasu nan iri -iri kamar su :-.. 


Mai Kan Tasa 

Mai Bakin Aku

Babba Da Jaka 

Mai kirar Mangoro

Yan Biyu na Gugar juna

Mai kudu da Arewa da sauransu.


Koma wani iri ne a kirjinki mijinki yana sha'awar ganinki dasu, shi yasa ma watakila ya aureki dominsu, don haka ya zama wajibi ke kuma ki kular masa dasu sosai da sosai.

Wasu mata nada jahilcin cewa, idan mace tana yawan shayarwa nono ta suna iya kwanciya da sauri. wasu matan ma cewa suke muddin mace tana barin mijinta yana yawan wasa da nonuwanta suna iya kwanciya tun ma bata tsufaba.


Tabbas haihuwa tana iya jawo nonuwan mace su kwanta, sai dai kuma a yadda kimiyya na zamani ya shigo a yanzu, mace tana iya haihuwa 'ya'ya dozun ba tare da nonuwanta sun kwanta ba. Kuma tana iya mikar da nono nata bayan ta gama haihuwa ko kuma a duk lokacin da take bukatar yin haka.


A yanzu haka likitoci na zamani sun samo hanyoyi da dama domin ganin mata masu sha'awan ganin sun tsufa da nonuwansu sunyi amfani dasu. Wasu kwayoyi ne na hadiya, wasu man shafawa ne, wasu kuma aikin tiyatane ake yiwa mace na irin duk yadda take bukatar ganin nonuwanta sun kasance.

Sai dai kuma duk matan da ta yanke shawarar gyara nonuwanta ta wadanan hanyoyin, ya zama dole ta tuntubi likita ne domin samun sha'warar irin wanda zai dace da ita domin kaucewa daga samun wata illa na rashin neman shawaran.


Duk da yake kyaun nonuwa halitta ne na Allah mahalicci, baya ga kuma hanyoyin kimiyya da masana suka gano na yadda suke gyara ko kwaskwariman nono a yanzu, da akwai kuma wasu hanyoyin da mace takan iya binsu domin kula da nonuwanta kamar haka:-


1) CIN ABINCI MAI KYAU:- Duk macen da take samun abinci mai kyau mai gina jiki tana iya gyaran nonuwanta ta wannan hanyar, domin duk tsufar mace muddin tana koshi da abinci, kuma cikin koshin lafiya, tana iya tsufa da nonon ta a kirjinta. Yana da kyau mata su rika cin abinci masu gina jiki irinsu kayan marmari, madara, kifi, nama da ire irensu.


2) KULA DA GIRMAN JIKI: Dole ne macen da take bukatar ganin nonuwanta suna da kyau ta kaucewa yin girman jiki sosai, haka kuma kada ta bari ta rame. domin wadannan abubuwa biyu idan suka yi yawa suna jawo dalilin zuban noni a kirjin mace. Domin yin kiba yakan jawo fatarki ta sake, wanda hakan kuma zai jawo dalilin kwanciyar nonuwan naki. Rama kuma yakan jawo rashin fatar da zata rike nonuwan har agansu a tsaye. Don haka wadannan abubuwan biyu dole mata su kula dasu muddin suna bukatar tsufa da nonuwansu.


3) RIGAR NONO: Dole ne mata su rika la"akari da irin rigunan nono da suke amfani dasu, kada ki rika amfani da rigar nonon da ya matseki, haka kuma kada ki rika sanya wanda ya miki kadan, domin hakan yana jawo jijiyoyin dake rike da nonuwan su saki ko kuma su kasa rike nonuwan yadda zai yi kyan gani.


4) MOTSA JIKI: Wasannin motsa jiki suna karawa mai yinsu lafiya, haka kuma yakan sa nonuwan mace su zama da kyaun gani, domin a kullum jini yana samun damar kewayawa a jikin macen da take yawan motsa jiki. Musamman ninkaye da wasu 'yan sarsarfa bana takura ba. Haka kuma idan kina iya maida hannayenki ta bayanki ki turo kirjinki gaba, kiyi haka a kullum kamar sau biyar, hakan yana karawa jijiyoyin nonuwanki karfi da kuma gewayawar jini anan, ta bakin wata mai aikin motsa jiki ga mata. Shi kansa tausa ga mace wani hanya ne dake karawa nonuwanta kyau.


5) WANKA:- Yin wanka da ruwan zafi bashi da kyau ga macen dake fatan ganin ta tsufa da nonuwanta. Domin ruwan zafi yana rage karfin fatar mace wanda hakan na iya jawo nonuwanta su zube da sauri. Sai dai wanda da ruwan dumi shi yafi mai makon ruwan zafi.


6) KWANCIYA: Babu kyau mace ta rika kwanciya a ruf da ciki yadda zata danne nonuwanta, hakan yana yiwa nonuwan mace illar da zai yi saurin zuba. Haka nan kuma yawan bayyana nonuwanki cikin rana shima yana jawo saurin zubansa, don haka mata su rika kaucewa yawan bayyana nonunwasu ciki zafin rana.


7) YAWAN SHAN RUWA:-Ki zama mai yawan shan ruwa wannan shima zai taimaka miki sosai domin ganin kin tsufa da nonuwanki. 


Idan hali yayi zamu zo da Bayanan kalolin nono da hotunansu a darasi na gaba idan Mai duka ya bamu iko. Ku kalli wannan VIDEO don jin cikakken bayani kan abinda muka tattauna. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post