Saƙon kalaman So Ga Budurwa Mai Ratsa Ruhi |
Saƙon kalaman So: Bana ganin kyawun kowacce budurwa sai kyawun ki, ke kadaice sarauniyar su,
Amincin Allah su kara tabbata agareki YAKE ma'abociya kamun kai nutsuwa hankali da ilmi, da fatan kina lafiya da aminchi mai dorewa.
Zuciyata cike take da tsananin kaunarki, bana iya tunanin kowacce budurwa sai ke, kece cikon farin cikin, ke kadaice Kyawun ki YAKE burgeni Kwalliyarki take burgeni, Murmushinki YAKE burgeni Adon ki YAKE burgeni,Tafiyarki take burgeni.
Bana ganin kyawun kowacce budurwa sai kyawun ki, ke kadaice sarauniyar su, tauraruwarsu dukkan yan mata sai dai su tsaya a gabanki su koyi kwalliya tsafta da iya zama da mutane lafiya, iliminki shine babban abinda ya jawo hankali na izuwa gareki.
Gaki da tarbiya INA tsananin sonki my blood, Allah ya sakawa iyayenki ko Nace iyayanki da sakamakon gidan aljannah bisa ilimi da tarbiyar da suka baki kowa yabanki YAKE, gaki da rikon amana babu ruwanki da San kudi irin na ƴan matan zamani, gaki da tausayi da karamci kome kin iya,
- Kin iya kallo
- Kin iya tafiya
- Kin iya murmushi
- Kin iya dress
- Kin iya mgn
- Kin iya kome
Bana iya kallan kowacce budurwa sai ke, duk yan mata kallan maza nake musu kin samu nasarar tafiya da duk zuciya ya ke tauraruwar da haskenki baya dushashewa, INA ji dake kece sirrin zuciyata, kece cikon farin cikina babu ruwanki da kula mazan zamani kanki a kame yake ,gaki da kula da addini,
- Ina sonki
- Ina kaunarki
- Ina begenki
- Ina shaukinki
- Ina muradinki
- Ina mararinki
- Ina kishinki
Ki huta lafiya sarauniyar ƴan mata kinfi dukkan ƴan mata kyawawan abubuwa na alkhairi my heart, Allah saka miki da alkhairi ki huta lafiya abar ƙauna.