Sakon So Gareka Abin Kauna Ta - Android Pols

Aisha Najamu: Sakon So Gareka Abin Kauna Ta
Sakon So Gareka Abin Kauna Ta  


Na kasa Bambance tsakanin Numfashi na da Kaunarka, shin wannene yafi Muhimmanci a gareni


Haske ya bayyana cikin kyakkyawar yanayin da zuciyata ke hasashen ganin sa cikin kala da nau'in dake kawata zuciyar duk wani ma'abocin so da kauna. 


Sahibi na, ko kasan yadda na shiga wani yanayi? Yanayi irin na farin ciki da haiban so?To yau da sanyayin safiya iska na kadawa cikin salo da sassayar muryarka ma'abocin taushi da tausasawa kake re romin kalaman soyayya wanda tasirin su ya rikita zuciyata. 


Lafazin kalaman bakinka suka jefa ruhina cikin shaukin So da KAUNA, Shiyasa kullum nake alkintaka a matsayin ma'abocin iya sarrafa zuciya, I love you masoyina. 


"Na kasa Bambance tsakanin Numfashi na da Kaunarka, shin wannene yafi Muhimmanci a gareni. Zuciya ta tana rasa Nutsuwa idan banji muryar ka ba abin kaunata. Dafatan ka tashi lafiya.


To be honest namiji na bukatar kulawa da bashi lokaci. Duk da ance su maza ba su fiya samun lokaci ba, amma duk rashin kulawa ne da basa samu daga wajen masoyiya. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post