Abincin Da Yaro Ya Kamata Yaci Don Kara Kaifin Basira |
Masana Sun Bayyana Abincin Da Yaro Ya Kamata Yaci Don Kara Kaifin Basira Da Lafiya
Abincin dake kara kaifin basira A al’adance musamman a kasashen mu na Hausa bamu cika baiwa yara abincin dake kara kaifin basira da fahimta ba. Asali irin abincin da muke yawan basu abinci ne nau’in (carbohydrate) wanda babban aikinsa a jikin yaro shi ne ya samar da karfi ga jiki. Cikin nau’ikan abincin da ake bukatar a dinga baiwa yara sun hadar da:
Abin da ake bukata anan shi ne a bawa yaro balance diet, kada a bawa yaro abinci kala daya dan dandanon dake ga wannan nau’in abincin.
Lokuta da dama zaka ga yaro da koshin lafiya amma kuma bashida fahimta a yanda ya dace ko kaman sauran yaran da suka taso, duk da yake ita basira da karfin kwakwalwa hikimomine na Allah.
Sai dai kuma kamar yadda muka san cewa dole sai an ci abinci ake samun jini wadatacce a jiki, kuma sai anci ake samun karfin jiki, to haka ita ma kwakwalwa da irin abincin da take bukata wanda idan aka dage da cinsa hakika za'a ga amfaninsa.
Muhimman Abincin Da Yaro Ya Kamata Yaci Don Kara Kaifin Basira
Binciken wasu likitoci sun lissafo abincin da zai taimakawa yaro wajen kara karfin kwakwalwarsu. Sun ce karancinsu na hana yara gane ko kuma fahimtar abin da ya kamata su gane musamman wajen karatu. Saboda hakan ne suke kira ga iyaye maza da mata da su tabbatar yaran su sun sami abinci kamar haka:
Kwai (Egg)
Cin dafaffen kwai, akwai wasu da suka camfa cewa baiwa kananan yara kwai, inda suke cewa idan yaro na cin kwai idan ya girma yana iya kasancewa yaro mai halin bera. A don haka basa baiwa yaransu kwai har sai sun girma. wannan camfi ne irin na Bahaushe amma ba kamshin gaskiya a ciki.
Don haka a dinga dafa kwai guda daya ya ana baiwa yaro a duk bayan kwan biyu. A cikin kwan, da akwai wasu sinadirran da zasu tallafawa kwakwalwa.
Cin ganyayyaki kamar su karas, alaiyahu, tumatur da sauransu. A koyawa yaro cin ganyayyaki ko da baya so saboda zasu amfane shi. Domin shi yaro baisan abinda ke amfanarsa ba, yafi son yaci abinci yaji zaki a bakinsa.
Kifi (fish)
Wannan zai fi dacewa idan aka yaye yaro, a nemi kifi mai kyau kuma wanda ya soyu, domin a mafi yawan kifin da ake sayarwa zaka tarar baya soyuwa wanda cinsa a haka yana haifarda tsutsar ciki ga yaro. zai fi kyau a dafa kifin sannan a baiwa yaro. wannan ba basira kadai zai kara ba harta da karfin sinadirran garkuwar jiki (immunity).
Madara (Milk)
Madara na dauke da sinadarin ‘Vitamin B’ wanda ke taimakawa wajen bunkasa kwakwalwa. Sai dai kuma zaifi kyau idan za a rika sarrafa madarar misali a sanyata a cikin kamu na gero a gauraya a baiwa yaro ya sha. kada a cika sukari a ciki, yawan shan madara ko kayan zaki na iya haifarwa yaro da basir. Amma idan aka sarrafata za a samu damar daidaita sinadiranta ta yanda ba za ta cutar ba.
Zuma (honey)
Yana da kyau a nemi zuma mai kyau ba wacce aka gauraye da sukari ba. Sai a rinka lasawa yaro kusan a kullum a kalla sau daya da safe.
Ruwan Kwakwa:
Baiwa yaro kwakwa yana ci ko ruwanta sai ya dinga sha. A hakika har lafiyar ciki da jiki zata kara bama kwakwalwa kadai ba.
Cin Kayayyakin Lambu:
Cin kayan lambu na taimakawa yaro Karin lafiya, Kamar su lemu, kankana, ayaba, abarba da ayaba suma abincin kwakwalwa ne masu samar da ishashiyar lafiya.
Dabino(date):
A baiwa yaro dabino yana ci shima yana da wata fa’ida ta daban musamman idan ana son ya yi saurin haddace abunda aka karantar da shi.
Duka wadannan ba wani tsada ke garesu ba sannan ba wai kullum take ci kala daya ba, a dinga yi ana canzawa. Ma'ana a yau idan an ci kwai gobe sai a ci kifi. Kuna iya kallon wannan video domin jin cikakken bayani kan irinsu nau'in abincin da ake baiwa yara.