Yadda Zaku Rabu Da Neman Matan Banza Bayan Kunyi Aure |
Maza Gareku: Yadda Zaku Rabu Da Neman Matan Banza Bayan Kunyi Aure
Babban matsalar da akasarin maza ma'aurata suke fuskanta bayan aurensu shine neman mata. Akwai wasu mazan da tun tasowarsu basu san wata mace ba ta hanyar Jima'i sai matan da suka aura.
Amma kuma bayan auren nasu sai kawai su ɓalle da neman matan banza ba ji ba gani. Haka kuma ana samun mazan da tun tasowar su da harkar neman mata suka tashi har bayan sunyi aure basa dainawa. Wanda wannan rukunin mazan su suka fi yawa. Irin waɗannan mazan akwai waɗanda suke neman hanyar su daina wannan baƙar dabi'ar ganin illarsa a garesu.
Sai dai cikin mazan da suke da dabi'ar neman matan banza ba dukkaninsu bane mazinata ba, duk kuwa da mazinantan sun fi yawa. Akwai mazan da kawai burinsu su kama tasha ne da matan da suke nema. Su riƙa yi musu hidima da sunan suna da 'yan mata amma ko inda take shanyar kamfenta bai taɓa gani ba.
Ba irin waɗannan mazan muke so muyi magana a kansu ba. Masu neman matan saboda zina a kansu ne muke son yin magana. Sai dai maza ma'aurata masu neman mata sun kasu kashi 4.
Akwai mazan da soyayya suke yi da matan da suke zina da su. Akwai mazan da babu ruwansu da soyayya su kawai idan sunga mace ta yi musu, su taya tayi farashin gabanta su biyata su kara gaba. Sai kuma mazan da su kuma wayo suke yiwa ƙananan yara musamman masu talla suke basu 'yan kuɗi kadan suyi lalata dasu.
Jerin mazan dake zina da mata bayan aurensu sune mazan da matan da kansu suke nemansu domin yin zina dasu, su basu da ɗabi'ar zuwa su nemi matan sai dai saboda wata baiwa ko ɗaukaka da suke da shi sai matan su da kansu suke shelantawa junansu baiwar wannan namijin domin yin zina da shi.
Irin waɗannan mazan sune ake samun matan dake biyansu domin su yi zinan dasu. Waɗannan jerin mazan guda huɗu masu neman mata da aurensu sune za muyi magana akansu, kuma kowanne mu kawo hanyoyin da mai yi zai iya dainawa kafin lokaci ya ƙure masa idan yana so.
Bari mu fara da mazan da suke soyayya da matan da suke zina da su.
Akasarin irin waɗannan mazan dai sune sukan jewa matan da sigar yin soyayya. Soyayya da tunanin zai aureta ko kuma soyayya da tunanin zai zama mai kula da duk wani ɗawainiyar ta amma babu zancen aure a tsakaninsu.
Da farko kafin namiji ya fara tunanin zai daina kula irin waɗannan matan da yake nema sai ya fara gano menene ya jawo masa neman irin waɗannan matan. Sai idan ya fahimci hakan ne sannan ma zai iya gano ta hanya ko hanyoyin da zai daina nemansu.
Akwai mazan da abokan da suke mu'amala dasu ne ke jefasu. Akwai mazan da irin yanayin muhallin da suka tsinci kansu a ciki ke sasu neman matan banza. Akwai kuma mazan da suna rasa wani ko wasu abubuwan ne daga matan da suke aure amma sai su samu waɗannan abubuwan a wajen wasu matan na banza. Da wannan ne za'a iya ɗaukan matakin da mutum zai daina idan ya gano abunda ke saka shi.
Mataki na farko, idan har abokan da kake tare dasu ne suke saka ka neman matan banza a waje da aurenka, dole ne ka ƙauracewa waɗannan abokan naka. Domin idan har baka binsu ko fita dasu inda kuke zuwa neman matan banza, ba za ka nemesu ba.
Ka samu wani abu mai mahimmanci da zaka maye gurbin lokacin da kuke zuwa neman matan banza tare da abokanka. Wannan abun kuma ya kasance abune da zai kusantar da kai da Allah, ko kuma abune da ya shafi neman kuɗi ko zumunci.
Duk lokacin da kayi tunanin amfani da wannan lokacin zuwa neman matan banza, sai kaga cewa wannan abun da kake yi yafi zuwa wajen matan banza muhimmanci nan take sai ka samu abun na fice maka arai, shi kuma abunda ka maye gurbinsa da shi yana ƙara shiga ranka.
Sannu a hankali sai ka soma fahimtar irin asarar da kake yi a harkar zuwa wajen neman matan banza, mai makon zama ko tsayawa kayi abinda kake yi a yanzu. Sai dai kuma wajen zullewa waɗannan abokan naka kana iya samun tirjiya daga garesu muddin kace musu ko ka nuna musu kai tsaye kai ga matakin da ka ɗauka na daina kula matan banza da ba aurensu zaka yi ba.
Domin shi abokin aikata saɓo a kullum yana baƙin cikin yaga abokan yinsa ya daina ko zai daina, don haka ne zaiyi ta iya yinsa domin ganin hakan bai yiwu ba. Wannan yasa a matakin farko kada kace zaka fito ƙarara ka nunawa abokan lalacewar naka ka fahimci rashin dacewar abinda kuke yi, ka samo wasu dabaru na noƙe musu sannu a hankali har lokacin da suka fahimci abinda yasa kake hakan da kansu.
Kuma idan ma sun gano kada ka soma yi musu bayani har sai idan sune suka buƙaci hakan. Idan har sun nema kuma kada ka tsaya yi musu dogon bayanin domin ƙoƙarin gamsar dasu. Kawai nuna musu rashin dacewar abinda kai kake yi ne ba abinda kuke yi ba.
Kada kayi amfani da kalmar (abinda muke yi bai dace ba). Ka kaɗaita lamarin a kanka har sai idan sune suka shigar da kansu a cikin rashin dacewar abinda kuke yi ɗin.