Matan Aure Gareku: Yadda Ake Yiwa Miji Idan An Kammala Saduwa

Matan Aure Gareku: Yadda Ake Yiwa Miji Idan An Kammala Saduwa
Yadda Ake Yiwa Miji Idan An Kammala Saduwa 


Yadda ake yiwa miji abubuwan dake ƙara masa nishadi da jindaɗi idan an kammala jima'i.


Da yawa daga cikin matan aure basu san yadda ake yiwa miji abubuwan dake ƙara musu nishaɗi ba. Akwai wasu abubuwa da ya kamata matan aure su dinga yiwa mazajensu musamman a lokacin da suka kammala jima'i. Ga abubuwan Kamar haka:


Yadda Ake Yin Tausar Maigida 

Bayan mijinku ya biya buƙata (relising), wani abu da za ki yi masa don ya samu cikakkiyar gamsuwa shi ne, ki ƙanƙame shi a ƙirjinki zuwa wani dan lokaci. Kalli wannan video don jin cikakken bayani sannan ki riƙa yi masa tausassan kalamai a kunnensa, lokaci zuwa lokaci ki riƙa yin wasa da harshenki a kunnensa, a lokaci guda ki riƙa yi masa raɗa a kunnensa. Sannan ki riƙa yi masa tausa, za ki yi masa tausa ne a gaɓoɓinsa da kuma wuraren da suke motsa sha’awa. Nasan matan aure da dama basu san yadda ake yin hakan ba sai yanzu.


A yayin tausar za ki iya yin amfani da yatsanki ko harshenki wajen yin wasa a kwarin bayansa, kwarin dunduniyarsa da wuyansa da kuma kwarmin bayan kunnensa, wannan yana sanya maza nishaɗi da sakewa bayan an yi jima’i, hakan kuma zai ba shi damar cikakkiyar gamsuwa.


Mafi yawan ƴan'uwa matan aure suna fama da matsaloli na rashin bada kulawa ga mazajensu, hakan tasa wasu mazan suke fara neman matan banza. Don haka ki kasance mai bawa mijin ki kulawa akan zamatakewar aure.


Wannan shine yadda ake yiwa miji idan an kammala jima'i. Da fatan matar aure za ki yi amfani da wannan damar domin ƙara farantawa mijinki rai da ƙara saka masa ƙaunarki a zuciyarsa.


Idan akwai matan auren dake buƙatar karin sani game da ɓangaren saduwa, gyaran matsalolin aure, matsalar soyayyah, ko ƴanmata da ake shirin aure zaku iya samun darussa da mukai akan su, idan kun latsa nan VIDEO.



Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

1 Comments

  1. AI Wani namijin bayason yayi magana ko ayi masa wata magana koda radace yayin saduwa da iyalinsa

    ReplyDelete
Previous Post Next Post