Matan Aure Gareku: Dabarun Yadda Ake Zama Da Kishiya A Gidan Aure

Matan Aure Gareku: Dabarun Yadda Ake Zama Da Kishiya A Gidan Aure

Dabarun Yadda Ake Zama Da Kishiya A Gidan Aure 


Dabarun Yadda Ake Zama Da Kishiya A Gidan Aure 


Rayuwar aure zama ne na hakuri, ba kowane lokaci ake samun yadda ake so ba. Idan mace tana da abokiyar zama a gidan aure dole ne sai sun yi hakuri da junansu domin dole ne irin wannan zaman sai ana samun matsaloli na yau da kullum.

Hakan yasa muka tattaro muku wasu daga cikin dabarun yadda ake iya zaman rayuwar aure da kishiya. Ga su kamar haka;


1. karki shiga hakkinta ko ya za’ayi, kiji tsoron Allah ki zauna da ita cikin aminci. 

2. ki sama ranki bata isa tayi maki komai ba face abunda Allah ya kaddara(ki rike Imani) kuma kisan cewa zaman aure kike. 

3.ki kasance mai bin dokan mijinki a koda yaushe. Domin rayuwar aure sai da bin umarni. 

4.Tsaftan jiki, gida, yara ki zamo gwana wajen iya tsafta. Duk matar da ta iya tsafta daban take da sauran mata. 

5. Karki yarda tasan abun da ke bata miki rai (Ko Rai YA Baci, Shiga Daki Kiyi Kuka, Ki YI Wanka Ki Dau Kwalliya)

6.Karki taba kai kararta gurin miji. Duk abinda za ta yi miki kiyi hakuri da ita, da kanta za ta gano Kuskurenta. 

7. ki zama kullun a cikin fara’a (Ba’a Da Kema Kishiya).

8. Kizama Kamar doki a gado (Ita kuma nunamata miji bai dame kiba)

9. Ki mata marhaba a farkon haduwa ku (Ko An Samu Matsala, Za'a ce Bake Kika Taba Tun Farko)

10. 'ya'yanki natane, karsu zamo kishiyoyinki.

11. Idan tamiki magana, karkiyi gaggawan ansata, bada kamar sec 30, kinga kin yi tunanani kuma zaisa tana shakkanki(AJI)

12. Iya Girki a rayuwar aure Babban Makami Ne. Ki yi kokari ki koyi girki. 

13. Ki zamo mai tattali bamai rowaba (Dabara) Ki cireta a ranki(BA ZAMANTA KIKEBA).

14. Ki zama yar kwalisa a kullun(Under12) Kar a gana ranar girkinki da akasinsa.

15. Ki rage yawan hira (Ke Ba Radio Bace). Ranan kwananki ke actor ce, ran nata boss(Rakashi da kiss mai zafi inzai tafi can). Kada ki nuna kishinki a fili.

16. Idan ya kiraki da sunanta, amsa, zai rasa abunda ya furta(In Ya Kira Ta Da NAKIt Masifa) ita ga sarkin yaki.

17. Kar kina magananta da wasu(Bata Dame Ki Ba)

18. Shagwaɓa amma a Daka.

19. komin zafin abu, baki ba dambe ko cacar baki da ita(Ke tsarartace?).

20. Yar Uwa Miji Sai Siyasa.

Wadannan sune daga cikin dabarun yadda iya zama da kishiya, da fatan matan aure kun ilimantu daga abubuwan da kuka Karanta.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post