Kalolin Abinci 6 Da Hada Su A Ci Ke Iya Zama Guba Ga Dan Adam |
Kalolin Abinci 6 Da Hada Su A Ci Ke Iya Zama Guba Ga Dan Adam
Ga mutanen da ke son hada nau'ukan abinci domin rage ƙiba da ƙarin kuzari ko mazakuta yana da kyau a fara tuntuɓar masana abinci.
Masaniya kan lafiyar abinci a Najeriya, Habiba Haruna, ta yi wa BBC bayani kan na'ukan abinci shida da idan an haɗa suke iya zama guba ga wani.
1- KIFI DA MADARA
Kifi da madara suna da sinadarai masu gina jiki kuma hade su wuri ɗaya ba zai karɓi wasu ba - zai iya zama matsala.
Wani yanayin jikinsa ba zai so sanadari iri daya ba kuma nau'i daban-daban idan suka hadu za su iya zama matsala.
Wani zai iya zama guba gare shi ya dinga yin amai wani kuma zai haddasa masa gudawa saboda hade nau'in abu biyu masu amfani iri daya a jiki.
2- MADARA DA AYABA
Haɗa madara da ayaba yakan iya zama guba ga wasu duk da cewa wasu za su hada su ci su kwana lafiya.
Ayaba tana da sinadarin potassium, idan mutum yana da ƙarancinsa kuma ya hada da madara ba zai samu matsala.
Amma wasu idan suka haɗa da madara da ayaba yana haifar masu da matsala kamar ƙaiƙayin wuya, wasu kuraje ko borin jini a jiki ko samiha.Wasu zai janyo masu kasala.
3- LEMON TSAMI DA MADARA
Madara da lemon tsami ba su shiri domin nan take madara za ta tsinke idan aka haɗa da lemon tsami.
Idan mutum ya hada lemon tsami da madara ya sha zai iya zaman masa guba. Zai iya sa wasu zafin zuciya.
4- GYADA DA MAN ZAITUN
Gyaɗa na da amfani sosai ga jikin ɗan adam kuma akan yi amfani da ita a fannoni da dama.
Gyaɗa na da sinadarin protein mai gina jiki da kuma sinadarin carbonhydrate mai kara kuzari.
Gyaɗa na cikin abubuwan da ke narkar da abinci, musamman masu son rage kiba suna amfani da gida a abinci.
Man zaitun kuma duk da yana da amfani musamman maganin cutuka da dama amma kuma hadawa da gyaɗa yana haifar da wani yanayi ga waɗanda ba su son man zaitun.
5- SHAN MAGANI DA LEMON KWALBA
Shan magani da wani nau'in kayan zaƙi mai gas kan iya haifar da mummunan illa ga mutum.
Masaniyar ta ce wani lokaci shan magani da Fanta ko Coca-Cola zai iya kashe mutum saboda gas.
Ta ce duk wani lemon zaƙi mai gas ba a son a hada da magani a sha.
6- DANYEN NAMA DA DANYEN KWAI
Haɗa ɗanyen nama da ɗanyen kwai zai iya haddasa matsala ga jikin wasu ƴan adam.
Yakan iya zama guba ga wasu, wasu na iya yin amai da gudawa saboda bai dace da yanayinsu ba.
Ɗanyen nama zai iya haifar da illa idan har ba a bi hanyoyin sarrafa shi ba domin rage karfin sinadaran da yake ɗauke da su.
Masaniyar ta ce ɗanyen kwai ba ya da wani amfani a jikin ɗan adam, domin yadda aka sha haka zai tsaya a jiki ba tare da wani amfani ba sai idan an dafa ko an soya ba. "Ba a aman ɗanyen ƙwai," in ji Ƙwararriya masaniya kan lafiyar abinci a Najeriya Habiba Haruna.
Masaniyar ta ba mutane shawara su ci abin da suka san zai masu amfani kuma ba zai haifar masu da matsala ba.
Kokarin gwada wani abu sabo zai iya amfani ga wasu amma kuma zai iya zama illa ga wasu.
Yadda ake da zabi da dama na nau'ukan abinci haka kuma yanayin mutane ya bambanta. Dole mutum sai ya yi taka-tsantsan da nau'ukan abincin da zai haɗa ya ci.