Kalmomin So Dake Ratsa Tunanin Masoyiya |
Kalmomin So: Son ki ya dade yana futar dani daga tunanin da yakamata ace nayi, yaushe zaki yadda cewa ina kaunar ki?
Ina sonki fiye da komai duk da bansan yadda rayuwata zata kasance ba wajen bayyana miki kalaman so.
Duk duniya babu abunda nake kauna kamar ki ammam sai dai ban son lokacin da zan ganki ba abar kauna.
Sonki yadade yana bani matsala a cikin rayuwata na yadda na aminta kaunarki ta zama silar ajalina dole na kasance cikin furta kalaman so da nake miki.
Son ki ya dade yana futar dani daga tunanin da yakamata ace nayi, yaushe zaki yadda cewa ina kaunar ki?
Amma yaya zanyi tunda kin zabi ki dinga azaftar da zuciyata abar farin cikin rayuwa ta.
Bazan iya bayyana miki yadda zuciyata ke sonki sama da yadda kika dauki so a cikin rayuwar ki
Duk fadin duniya bani da makiyi kamar sonki amma haka naji kuma na aminta dake a cikin kahon zuciyata.
Domin nasan wata rana kiyayyar da sonki ke mani zata rikida zuwa ta falkin kauna masoyiya.
Bansan halin da zaki shiga ba idan na bayyana miki yadda zuciya ke sonki ba, dole ne na dage wajen bayyana miki kalaman so dake zuciya ta.