Kalaman soyayya na gaskiya da gaskiya - Android Pols

Hadiza Gabon: Kalaman soyayya na gaskiya da gaskiya
Hadiza Gabon: Kalaman soyayya na gaskiya da gaskiya


Kalaman soyayya na gaskiya: Ina sonki saboda naganki na yaba da halayenki a irin yanayin dana ganki inafatan ki kasance hakan koda yaushe.


Ga wasu kalaman soyayya na gaskiya da gaskiya da masoya za su ke yiwa junansu. Don hakan zai ƙara inganta ƙaunar juna da kuma yarda a zamantakewar aure da soyayya juna.


Kalaman So Zuwaga baiwar Allah 

Assalamu alaiki ƴan mata sallama mafarin kowani alkhairi ina fatan wannan sallamar tawa ta zamo farko cikin miliyoyin sallamata a gareki.

Nayi nazari dogon tinani da hangen nesa gameda baiwar Allah dana gani naji inason hada alaka da ita ta soyayya.

Tabbas ke kyakkyawa ce amma ba zan ce ban taba ganin kyakkyawa kamarkiba ko kuma wacce tafiki ba sai dai ke dince kikafi kwanta min arai har naji inasonki.

Ke din ta musammance ba zance miki bantaba soyayya ba nayi soyayya da ƴan mata sosai amma ina fatan soyayyata da taki tayi ɗorewa ta har abada.

Ina sonki saboda naganki na yaba da halayenki a irin yanayin dana ganki inafatan ki kasance hakan koda yaushe.

Ina sonki amma zan iya rayuwata sarai ko bake inafatan kiyi nazari da lissafi wajen amsar soyayyata domin bana ƙarya dan a soni.

Bazan iya kiranki da sarauniya ba domin ke ɗin baki riga kin zama tawa ba amma inada tabbacin zaki zama yar gata agareni shalele zakiyi farinciki irin na masoya har abada.

Sunana iliyasu wasu sukan kirani da Any boy amma zanso ki lakaba min wani suna me ma'ana na masoya domin jindadin kasancewata dake.

Zan tsaya anan badan na ƙarasa zayyana miki abunda ke zuciyata ba se dai dan na taƙaita rubutuna agareki ina jiran amsa daga gareki abar ƙaunata a soyayya.

Ina sonki ban riga na fara kaunarki ba, Ina yawaita tinaninki amma ban riga na fara mafarkinki ba, Amma inaso nakai wannan matakin a soyayyarki baiwar Allah .

Senaji daga gareki 

Kuna ganin zan idan saurayi yana yiwa budurwa waɗannan kalaman so zai samu karbuwa kuwa a wajen wannan baiwar Allah? Ku bayyana mana ra'ayoyin ku.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post