Kalaman Soyayya Masu Rasta Zuciyar Budurwa - Android Pols

Aisha Humaira: Kalaman Soyayya Masu Rasta Zuciyar Budurwa
Kalaman Soyayya Masu Rasta Zuciyar Budurwa 

 

Kalaman Soyayya: Kaunarki ce mafari kuma silar wanzuwar duk wani farinciki ko haske acikin duniyata


A duk lokacin da tattausan lafazinki ya tinkari kofar zuciyata da zummar isar da sakon farincikin dake zuciyarki, sai inji daddadan shaukin da burina ya mallaka sanadin kamuwa da kaunarki yazo tarbarshi adai dai gabar gangar jiki da kuma burina, haka wannan kwakkwaran dalilin shine mahadin kwarin gwiwar da tasa nakeji ajikina ke watace domin bada iya zuciya kadai nake kaunarki ba, harda jinki a rainama. 


Kaunarki ce mafari kuma silar wanzuwar duk wani farinciki ko haske acikin duniyata, domin annurin amin tacciyar zuciyarki ne mahadin ko ince cikon mafarkin farincikin zuciyata a ko yaushe.


 Allah sarki zuciyata haka nakanji tausayin kaina a bisa yanda naga zuciyata tana rarraba aikin kaunarki izuwa sassan jikina, domin tum kafin aje ko ina har nakai matakin bazan iya rayuwa babu ke ba. 


Ina da tarin burika a cikin rayuwata amma mallakar zahirin mafarkin sace zuciyar kyakykywar gimbiyata shine rubutun da zuciyata ke iya karantawa a ko yaushe, kuma shine karatun da bakina yake mai maitawa a yanzu haka. 


Indai har zuciyata zata iya samun farinciki sanadin gani ko jin haddaddiyar lallausar muryarki, to mai zai hana zuciyata zumdin son kasan cewar zuciya tafarko da kyakykywar zuciyarki ta sahalewa sahannu yar jejeniyar rayuwa da ita ta har abada. 


Nauyin furuci ko fadin cewar ke kyakykywace ba'a iya wuyana kadai ya rataya ba, haka wannan nauyin ya rataya ne a wuyan duk wanda ya samu nasarar yin tozali da kyakykywar fuskarki bugu da kari ace kin bayyana kyakykywar murmushinki a kolacin. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post