Kalaman Soyayya Masu Rasta Zuciyar Budurwa |
Kalaman Soyayya Masu Rasta Zuciyar Budurwa
Bayyanar sallama ta agareki nake sa ran ya zamo silar farantawa zuciyarki, amma amsa kyakkyawar sallama mai cike da salamar faranta ruhinki ne kadai zai sa zuciyata ta gamsu cewa sakona yazo gareki abar kaunata.
A iya sanina dai a jikin zinariya ake sa ran kyalkyali haka zalika kuma ajikin tauraruwa ake sa ran ganin haske, amma sai ga wata sarauniyar rayuwa ta samu duk wanannan abubuwan a tattare da ita, matukar kin kasance haka, dole ne zuciyata naiwa kyakkyawar zuciyarki tana din dadda-dan farinciki da shauni ko dan samun nawa farincikin, kin kasance tamkar dawisu a cikin tsunstsaye domin iya rayuwata ban taba tozali da kyakkyawar da ado ke yiwa kyawu ba tamkar ke sahibata.
Nakan jin tamkar na zauce a yayin da kyauki yake bayyana tahanyar bayyanar kyakkyawan murmushin kan fuskarki, da idanun zuciyata nake kallon kyakkyawar suffa da kuma zubin halittarki, ina kaunarki matuka zan so kice, "nimahaka masoyiya ".