Kalaman Soyayya Masu Rasta Jikin Masoya - Android Pols

Kalaman Soyayya Masu Rasta Jikin Masoya

Kalaman Soyayya Masu Rasta Jikin Masoya


Furta kalaman soyayya a tsakanin masoya na kara tabbatar da kaunar juna 


Idan masoya na furta kalaman soyayya a tsakanin su yana kara tabbatar musu da soyayyar juna da kara son juna. Ga wasu daga cikin Kalaman soyayya da ya kamata masoya su dinga furtawa junansu kamar;


Amnci ya tabbata a gareki yake hasken zuciyata, aminci ya tabbata agareki yake hasken rayuwata, aminci ya tabbata agareki yake farin cikin zuciyata, aminci ya tabbata agareki yake sarauniyar dake mulki a cikin zuciyata.  


Soyayyarki wani haskene dake haska rayuwata, soyayyar ki wani nau'i ne dake sakani farin ciki da annashuwa, soyayyar ki wani launine dake sakani walwala da ta kama, soyayyar ki wani abune dake sakani zumudi da annsuwa. Wadannan kalaman soyayya ne masu rasta jikin masoyiyarka.


Kallonki yana karamin gani, kallonki yana karamin Sonki, kallonki yana karamin shauki da soyayyar ki, kallonki na kara sakani naji kamar babu wanda yakaini dace, kallonki na kara sakani shiga duniyar Sonki, kallonki yana karamin kara sonki, kallonki nakara sakani naje karfin guiwa yake yar aljanna. 


Zan jure komai a kanki, zan jure kin cin abinci da kin sha, indai banji muryarki ba zan iya kin motsi da kin sha da kin ci, indai hankalinki zai bace ranki zai bace, zan jure zama ni kadai naki yin magana, indai har bakyanan zan iya fidda komai akanki zan iya jure zafi da radadi akanki yake farinchikina. 


Ban taba ganin wadda takaikiba kuma bazan ganiba, bantaba son wata ba indai bake ba, kuma ba zan taba so ba, bantaba tsayawa da wataba indai bake ba kuma bazan tsayaba bantaba zaunawa nai hira da wataba indai bake ba, kuma bazan aikata hakanba saboda ina kishinki. Kalaman soyayya ne da mata ke so 


Indai zanganki kina farinchiki zanji duk duniya babu wanda yakaini jin dadi indai har zan ganoki kina tafiya kina fara'a da bakinki me kyau da dogon hancinki tofa zan dinga jin zuciyata da numfashina na fita daidai kamar ina tare dake, indai har zanji muryarki zan jure zama har kigama magana, indai har zanji motsinki zanzauna har naganki, domin zuciyata ta samu salama da natsuwa. 


Kallonki yakan saka ni nishadi kamar yanda yabanki yake saka zuciya annshuwa, kalonki cikin farinchiki yana kwantarmin da zuciya kamar yanda kallonki chikin fushi take tayarmin da hankali na, kallonki kina fara'a shi ke sakani fara'a kamar yanda kallonki kina daure fuska yake tada hankalina yake sarauniyar mata. 


Rashinki babbar asarace agareni kamar yanda samunki babbar nasarace agareni kalonki babbar kima ce aguna kamar yanda rashin ganinki babban tashin hankaline a guna yake wahainiya sarauniyar iya tafiya. Mace na son irin wannan Kalaman soyayya. 


Kin iya komai kamar yanda kika iya karatu, kin iya kwalliya kamar yanda kika iya girmama manya, kin iya tafiya kamar yanda kika iya daukar wanka, kin iya murmushi kamar yanda kike tsarawa kanki rayuwa me kyau yake annurin zuciyata. 


Zan baki farin ciki wanda ba'a taba baiwa wata ya mace ba a duniya zan zamar maki gata wanda za kiyi takama dani na har abada, zanbaki farinchiki wanda zaki alfahari dani na har abada zanbaki duk wata kulawa wadda ba'a taba bawa wata ya mace ba. 


Samunki baban nasarace arayuwa ta kamar yanda rashinki babbar asarace aguna ina kaunarki sosai, ina sonki sosai yake yar aljanna.


Wannan wasu Kenan daga cikin Kalaman soyayya dake firgita mace idan namiji yana furta mata su. Sai dai Kash ba kowane namiji ne ke iya yiwa macen da yake so irin wannan kalaman ba. Har idan kana son ka mallaki zuciyar mace ka dinga yi mata irin wadannan kalaman. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

1 Comments

Previous Post Next Post