Kalaman Soyayya Masu Dadi Da Ratsa |
Idan baka iya yiwa mace Kalaman Soyayya ba to tabbas za'a barka a baya Wurin iya Soyayya, Wannan ita ce Magana ta Gaskiya
Shin kana cikin Samari Masu neman Budurwa wadda zasu aura? Ko kana SHAN wahala wurin tsayar da budurwa da kake so ka aura? Ko kuma baka san irin kalaman soyayya da za ka iya shawo kan budurwa ba?
Nasan soyayya itace take ranka wannan yasa kake karanta Wannan rubutun. To idan Kana Soyayya kuma kana cikin Samari Masu yin Soyayya Yana da kyau duk Saurayi Yasan Cewa Budurwa Sai da Kalaman Soyayya. Idan baka iya yiwa mace Kalaman Soyayya ba to tabbas za'a barka a baya Wurin iya Soyayya, Wannan ita ce Magana ta Gaskiya,
Domin sau da dama ansha amshe ma saurayi Budurwa ta dalilin rashin iya kalaman soyayya. Wannan ne yasa Muka Tace, Muka Darje, Muka tsara muku Kalaman Soyayya Masu Dadi da Ratsa jikin Masoya. Gasu a nan kasa Asha Karatu Lafiya.
- Abubuwa kaɗan ne suke da daraja a wurin a cikin wannan duniyar, ɗaya daga cikin su shine Murmushi ki, my priceless gift.
- Gari ya Waye, sabuwar rana ta fara, Ina Farin ciki da Nishadi saboda ina da ke a cikin rayuwata.
- Ina jin Soyayyar ki Wata Kyauta ce agareni da ban taba samun kyauta irin ta ba a rayuwata, my super lady.
- Na dade ina kallon taurarin samaniya yayinda naga wacce tafi kowacce haske, sai naga bakowa bace nike gani ba sai ke masoyiya ta.
- So gamon jinine, hakika sonki ya zamo jinin jikina, Ki kwantar da hankalinki masoyiyata babu wata a zuciyata sai ke kadai.
- Congrats to me, saboda na Samu Mafi kyawu, Kulawa da Yarinyar da take Saurin Fahimta ta, kuma kece, my love. Yarda da amincewarki gareni, sune zasu tabbatar da soyayyarki ta gaskiya a gareni.
- Yau nayi mafarki, Kin kawo mini ruwa mai sanyi tare da wani a hannun ki, wannan abun kuwa shine soyayya ta dana baki, ki riƙe shi kada ki sake.
- Farin ciki baya dorewa a rayuwa sai tare da bakin ciki, dan haka kowane hali nike bazan taba mantawa dake ba masoyiya ta.
- Da Farko Ina Miki Sallama Irin Wacce Na Saba Miki a Kullum, Sannan Ina Miki fatan Alkhairi irin wanda na saba a kullum, kin tashi lafiya, Ya zuciyar ki take? Ta kasance lafiya, ko ta kasance kullum cikin tinani na.
Wadannan sune wasu daga cikin kalaman soyayya masu dadi da ratsa jiki da ya dace duk wani namiji ko saurayi ya iya furtawa budurwarsa ko matarsa su. Allah yasa mu dace Amin.