Kalaman Soyayya |
Wadannan Kalaman Soyayya Ne Masu Kara Dankon Soyayya Ga Masoya
Assalamu Alaikum Warahamatullah, Yan’uwa barka da wannan lokacin haka da farko zance duk lamarin da zaka gina to ka ginashi akan turba ta Gaskiya domin shi kalaman soyayya gaskiya ne, amma marasa gaskiya kan shigeta har su ɓatata kuma su tozartata.
Nayi nazari akan wasu kalamai na soyayya amma ga wanda yasan zaiyi soyayya ta nufin yin Aure ba ta yaudara ba. Indai da nufin aure kake son mace tabbas waɗannan kalaman soyayya zasu tai maka maka matuƙa.
Kada ka ɓata lokacinka ga soyayya da babu nufin aure a cikin ta koda kayi baza kayi nasara ba, kuma kaima sai anyi da ɗiyarka. Anya zaka so a yi maka ɗiyarka ƙaryar soyayya? Nasan mai karatu ba zai so haka ba, to kada kayi Dan Allah.
Yadda Za Ka Furta Wa Budurwa Kalaman Soyayya
Furta kalaman soyayya ga budurwa ko saurayi yana da matuƙar muhimmanci domin yana ƙara soyayyar juna tsakanin masoya. Idan kana tare da budurwa / masoyiyarka, yana da kyau ka kasance kanayi mata kalaman soyayya masu dadi na jan hankali, waɗanda zasu dinga faranta mata rai.
Domin babu abinda yafi jan hankalin mata kamar kalaman soyayya. Matukar Baka Yin Kalaman Soyayya to Anbarka Abaya. Daga Cikin Kalaman Soyayya da ake furtawa masoya sune kamar haka;
Na dade ina kallon taurarin samaniya yayinda naga wacce tafi kowacce haske, sai naga bakowa bace nike ganiba sai ke masoyiyata.
So gamon jinine, haqiqa sonki ya zamo jinin jikina ta yadda ya mamaye zuciya ta bana tunanin kowa sai ke.
Kinfita daban a cikin mata, duk lokacin da na kallleki, sai naga kamar babu kyakykyawar mace sai ke. Ki kwantar da hankalinki masoyiyata babu wata a zuciyata sai ke kadai.
Yarda da amincewar ki gareni, sune zasu tabbatar da soyayyar ki ta gaskiya a gareni. Farin ciki baya dorewa a rayuwa sai tare da bakin ciki, dan haka kowane hali nike bazan taɓa mantawa dake ba masoyiyata.
Nakan raba dare ina mai roƙon Allah (S.W.T) don neman biyan buƙata, ko kinsan kece abu na farko da nike roƙon samu.
Soyayya: Manya Manyan Kayataccin Kalaman Soyayya na Sace Zuciya
Domin Masoya Masu Soyayya.
ﻗﺪﺭﺕ ﮔﺮﻓﺘﻪ ﺍﺯ ﺍﻓﺰﻭﻧﻪ ﻧﻮﺷﺘﻪﻫﺎﯼ ﻣﺮﺗﺒﻂ ﻫﻮﺷﻤﻨﺪ
Yanayin sanyi kan sa mutum ya takura, tare da lulluɓe da ƙaton mayafi amma ni duk sanyin da ake idan na tunaki sai naji tamkar yanayin zafi.
Kamar yadda kowacce bishiya kanyi rassa a sama, kuma tayi saiwa a ƙasa, haka sonki ya mamaye dukkan jikina, Idan na kalleki sai nayi farin ciki, idan naji tattausan muryar ki, sai nishadi da walwala tare da annashuwa gami da farin ciki su mamaye zuciyata.
Abokina a hakan zaka bi don sace zuciyar masoyiyarka cikin sauki, Siffar ki da halayenki sune abin yabawa ga duk da namiji musamman ni, ka fita daban a cikin mata na yarda da ke saboda kyakykyawar surar jikinki, ga kamun kai da sanin yakamata matama da irinki soke yin koyi wallahi ina Sonki.
Domin Mata: Kina Soyayya? Ko kinada Mai Sonki? Karanta Wannan Sakon
ﻗﺪﺭﺕ ﮔﺮﻓﺘﻪ ﺍﺯ ﺍﻓﺰﻭﻧﻪ ﻧﻮﺷﺘﻪﻫﺎﯼ ﻣﺮﺗﺒﻂ ﻫﻮﺷﻤﻨﺪ
Kalaman soyayya Zasu Iya Sauyawa zuwa Lamiri/Jinsin Namiji, Saboda Haka Kema zaki iya juya turn na wannan kalaman domin sace zuciyar masoyinki cikin sauk. Idan kuma kinyi musu ku jaraba kugani.
Daga Karshe Ina Son Mai karatu ya fahimci cewa Kalaman soyayya Suna tasiri ne kadai idan dama akwai so tsakanin saurayi da budurwa ko mata da miji, idan kasan babu so tun farko to kada ka bata lokacin ka. Allah yasa soyayya ce ta nufin ayi aure.