Kalaman So Na Sace Zuciyar Budurwa A Farkon Haduwarku

Kalaman So Na Sace Zuciyar Budurwa A Farkon Haduwarku
Kalaman So Na Sace Zuciyar Budurwa A Farkon Haduwarku 


 Akwai wasu halaye da ya kamata ka daina lokachin da zakaje wajen mace dan neman soyayyarta da kuma lokachin da ka zama wanda take so.


Yanzu lokaci ya canja an daina furtawa ƴan mata KALMAR SO a haduwar farko, lallai ne idan kana so kasamu karbuwa wajen mace to kasamu wata hanya wadda zaku ringa haduwa kuna fıra. 


A cikin fırar kada ka kuskura ka nuna mata alamomin So ka kyaleta zuwa gaba zata sani kayi kokarin sakata daria a lokacin da kuke tare, idan kuka fara shakuwa ka ringa nuna mata duk duniya ba kaga macen da ta tsaru ba kamarta amma kada ka zake a wannan fannin, Sannu a hankali sai ka fara aika mata text ta ido.


Kuma zuwa lokachin ka dan ringa tambayarta cewa Wai wane mai tsananin sa,a ne ya mallaki zuciyar wannan tsadaddiyar yarinyar? Idan har ta basar da zanchen tofa kachi gari ko kuma tace ma wani ne kuma taki fada maka sunansa to kai din take nufi.


Akwai wasu halaye da ya kamata ka daina lokachin da zakaje wajen mace dan neman soyayyarta da kuma lokachin da ka zama wanda take so. Ga su kamar haka;


1 Yawan tambaya:  mai wannan halayya ya kan fita daga zuciyar mata


2 kasani dole ne ka dan yiwa wadda kake so hidima koda kuwa ba aurenta zakayi ba, mata basu son marowacin saurayi kai da kanka ma tuni kasan kyauta na jawo shakuwa, Ita kuma shakuwa tana saka SO .


3 Idan ka tabbata ka zama wanda take so sosai to kaima sai ka dan ja naka class din, kilan kace meyasa to ka lura ko abinci ne kake kullum isarka zaiyi itama mace ai haka take


4 yanada kyau kwarai ka zama gwani wajen furta KALAMAN SO suma suna taka muhimmiyar rawa. Ka zama mai matukar tsafta, dan kuwa kamar yadda kake ganin yam mata idan sun dau wanka kaji sun birgeka, haka suma matan kalar waɗannan samarin ke birgesu.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post