Kalaman So Masu Daɗi Ga Budurwa |
Kalaman So: Kinsan cewa kinkai matakin canza ra'ayin zuciyoyi dadama sanadin iya ɗaukar wanka da kuma tsara kyakkywar kwalliyarki
Shin ka iya furta kalaman so ga budurwar ka, shin kalaman da kake yiwa abar ƙaunarka suna birgeta? Idan baka iya furta kalaman so ga budurwa ba ga wasu daga cikin kalaman so da idan kana furtawa abar ƙaunarka za ka ƙara shiga ranta.
Hhmm, abar kaunata shin ko kinsan yadda asalin kyakkywar surarki take bayyana a lokacin da kikayi ado.
Kinsan cewa kinkai matakin canza ra'ayin zuciyoyi dadama sanadin iya ɗaukar wanka da kuma tsara kyakkywar Kwalliyar ki.
Inaso ki sani cewa ke kaɗaice kyakkywar sauniyar da nake yiwa laƙabi da gwanar ado. Domin kin kasance me kalar samfarin kyawun halittar da ba'a cika samun irinku a kasar hausawa ba.
Zuciyata takan samu wadatacciyar walwala da shauƙi a duk lokacin da mai tozali da ƙayataccen adonki mai sanya farinciki yaiwa zuciyata saukar ungulu, kisanifa ke kaɗai ce me adon da zai zama abun kallo a gareni.
Waɗannan kaɗan ne daga cikin kalaman so ga budurwa wanda idan ana yi mata su za ta ƙara ƙaunarka da soyayyar ka a zuciyarta. Ina fatan samari za su dage wajen iya kalaman soyayya ga budurwa.