kalaman So Ga Saurayi Masu Zafi - Android Pols
![]() |
kalaman So Ga Saurayi Masu Zafi |
Kalaman So: A cikin rayuwata ka kasance jarumuin dake jagorantar zuciyata izuwa duniyar da ake samar da farin ciki da samun Kyakyawar kulawa
Budurwa shin kina da kalamai na so da idan kika furtawa saurayinki su yana jindadi da samun nustuwa? Idan bakida su ko kuma idan baki iya ba. Ga wasu zafafan kalaman so da za ki dinga furtawa saurayinki su.
(1) Uzuri zan yiwa duk wanda yace na makance akan kaunarka, domin kana da wata Kyakykywar baiwa wacce duk me ita a kalmar hausa sai dai a kirashi da Kyakykywa, watakila kai kadai ne mai rabon gane hakan a gareka Masoyina.
(2) Muradin sanka na sanya amin-tacciyar zuciyata a cikin shauki mai sanya dadda-dan yanayi shine kudurin zuciyata, domin farin cikin ka shine walwalar ruhina, kai na dabanne dole na kiraka da tauraro, kuma madubin duk idaniyar da take son yin tozali da Kyakykywa.
(3) A cikin rayuwata ka kasance jarumuin dake jagorantar zuciyata izuwa duniyar da ake samar da farin ciki da samun Kyakyawar kulawa, ina nufin duniyar masoya, me mulki ake kira da sarki karka dauka nayi aron kalma idan nakiraka da me mulkin zuciyata.
(4) Muradin zuciya zai kasan ce abinda take kaunane mu yi rayuwa kuma shine samun muradin zuciyata, to kamar hakane bayyanar dauwa mammiyar kaunaka ce silar son kasancewa tare dakai na har 'abada masoyin zuciyata.
Leave Comments
Post a Comment