Kalaman So Da Jan Hankali Na Sace Zuciyar Budurwa |
Tabbas idan dai har kana so ka yiwa mace satar zucciya dolene sai ka bi dokoki na yadda ake bayyana kalaman so masu ratsa zuciya
Tayayya zan sace Zuciyar Budurwa? Wannan itace tambayar da samari da dama ke yiwa Zuciyarsu. A gaskiya sace zucciyar mace abu ne mai sauki ga wanda ya gane sannan kuma abu ne mai wuya ga wanda bai gane ba.
Tabbas idan dai har kana so ka yiwa mace satar zucciya dolene sai ka bi dokoki na yadda ake bayyana kalaman so masu ratsa zuciya da saka tunanin budurwa a zuciyar ta. Ga abubuwan kamar haka:
1 Jan-Aji: ka sani fa budurwa bazata iya mallaka maka kanta hakannan kawai ba dolene sai ta ja maka aji dan ta gane halayenka da haƙurinka sannan kuma zata so ta gane ko da gaske ne kake sonta ko ba da gaske ba sabida mata sun tsani duk wani saurayin dake shirin yaudaransu. Idan har kaga ka zowa mace kai tsaye ta amince dakai ba tareda jan class ba, to fa ka tsoraci lamarinta domin mace idan har cikakkiyar gogaggiyar mace ce to zata ja maka class sosai har sai ka kusan yin kuka tukunna.
2 Hakuri: Tabbas dolene sai ka zamo mai hakuri idan ba haka ba bazaka samu damar lashe jarabawar da mace zata yima ba sabida zakaga ababe da dama masu gasa zucciya, idan har baka zamo mai hakuri ba; to kai da yin soyayya da mace saidai a slow.
3 Gaskiya: mace tafi son saurayin da ke gaya mata gaskiya kai tsaye, kada ka bayyana kalamar so ta karya gareta, idan har kai makaryaci ne to ina mai tabbatarma da cewa idan har tazo ta gane sirrinka zaka sha kashi, dan haka ake kwatanta gaskiya daidai gwargwado.
4. Kulawa: dolene idan dai har kana son zamanka da mace ya ɗauki tsawon lokaci kuma yasa ta soka sosai fiye da kima to lallai kuwa dolene sai ka kula da ita tamkar yanda zaka kula da kanka a lokacin da kake cikin rashin lafiya. Kulawa yana ɗaya daga cikin siffofin abinda mata suke so.
5. Rarrashi Tareda Girmamawa: Mace tafi so idan har ka sanyata yin fushi to ka rarrasheta tamkar yanda zaka rarrashi jaririya. Kuma mace zata ji daɗi sosai fiye da kima idan dai har kana girmamata, ta fannin yabon halayenta na kirki tareda nuna mata cewa babu wanda kafi so a duniya tamkar ita sabida tana da halin kirki.
Sannan kuma bayyana mata kalaman So na daga cikin abinda ke karawa mace kaunar namiji a zuciyar ta. Idan baka san yadda furta kalmomin soyayya ba ka yi kokari ka koya domin za su taimaka maka sosai wajen sace zuciyar budurwar ka.