Kafin Ka Yi Aure Ga Shawarari Masu Muhimmanci Guda 10 - Android Pols

Kafin Ka Yi Aure Ga Shawarari Masu Muhimmanci Guda 10

Kafin Ka Yi Aure Ga Shawarari Masu Muhimmanci Guda 10


Don Samari: Kafin Ka Yi Aure Ga Shawarari Masu Muhimmanci Guda 10


Aure muhimmin al'amari ne, kuma ba abin wasa bane. Aure abu ne mai daraja da ya kamata tun kafin a yi shi a san muhimmancinsa. Ga wasu daga cikin shawarwari da za su amfani matasa masu son yin aure nan gaba 

1) Kafin ka yi aure dole ka samu cikakken sani game da aure, ƙa'idoji da sharuɗɗan da Allah (SWT) ya shimfiɗa a cikinsa. 

2) Kafin ka yi aure ya dace ka samu ilimin yadda za ka mu'amalanci matarka gurin mu'amalar aure, don gudun faɗawa cikin jagwalgwalo. 

3) Dole ka san cewa kaine wanda Allah ya ɗorawa alhakin ciyar da iyalinka, ilmantar da su, tufatar da su da nema musu lafiya a lokacin da suke cikin rashin lafiya

4) Ya zama dole ka samu cikakkiyar sana'ar da zaka iya ɗaukar duk wata ɗawainiyar iyalanka kafin kayi aure. Addini ma bai yarda wanda ba zai iya ɗaukar nauyin iyali ya yi aure ba. 

5) Idan kana son ɗorewar zaman aurenka, to sai ka samu kyakkyawar niyya game da auren, ba don sha'awa kawai ko dan abokanka sun yi aure kaima za ka yi ba. 

6) Ya dace ka bayyanawa wadda zaka aura ainahin ɗabi'unka, kar ka ɓoyewa wadda zaka aura ɗabi'arka, idan ɗabi'ar mara kyau ce, sai kayi ƙoƙarin gyarawa. 

7) Kada ka nunawa wadda zaka aura kai mai wadata ne alhalin ba haka abin yake ba, ka nuna mata gaskiyar yadda kake, idan taƙi akwai wadda zata so ka a yadda kake. 

8) Ya dace ka fahimci ɗabi'ar wadda zaka aura kafin ka aureta, domin ka san yadda za ka zauna da ita. 

9) Kada ka yi doguwar soyayya kafin aure, idan kuka fahimci kuna son junanku kuma kun fahimci junanku sai kuyi aure, doguwar soyayya tafi kama da yaudara. 

10) Ka nunawa macen da zaka aura kana girmama iyayenka da ƴan uwanka, kuma kaima ka girmama iyayenta da ƴan uwanta.

Wannan sune Muhimman shawarari 10 da ya kamata ku sani kafin ku yi aure. Ya Allah kabamu abokan zama nagari, ka bamu ikon kyautatamusu, suma ka basu ikon kyautatamana ya hayyu ya kayyum.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post