Illolin Talla Ga Rayuwar Ƴan Mata -Android Pols

Illolin Talla Ga Rayuwar Ƴan Mata
Illolin Talla Ga Rayuwar Ƴan Mata 


Illolin Talla Ga Rayuwar Ƴan Mata Da Irin Hatsarin Da Mata Ke Shiga A Dalilin Talla


Sana'ar talla tana da illoli masu ɗunbin yawa ga rayuwar mata musamman wanda sun kai munzalin yin aure. 


A mafi akasin garuruwan jihohin Arewacin Najeria, yana da wuya kayi tafiyan minti guda baka ga ƴan mata suna talla ba; a bakin kasuwa ko makaranta, tasha ko masana'anta, wureren leburori ko kan titi, gidajen kallon kwallo ko sinima, filin kwallo ko gidajen dambe, babu dare babu rana.


Babban abunda zai baka mamaki shine, yawancin abubuwan da suke sayarwa basa wuce abun Naira dubu ɗaya zuwa dubu biyar, amma yarinya zata bar gidan iyayenta tun da safe har zuwa dare da sunan talla.


Mafi muni shine, wasunsu har lunguna suna shiga da katti da sunan talla. 


Illolin Talla Ga Rayuwar Ƴan Mata sune;

  1. Talla tana kawo fyade har ta kai ga taɓa mutuncin ƴa'ƴa mata, 
  2. Talla yana hana ƴa'ƴa mata sallah a kanl okaci, 
  3. Talla tana hana ƴa'ƴa mata karutu (na addini ko boko), 
  4. Talla tana ɓata tarbiyyan ƴa'ƴa mata, 
  5. Talla saka ƴa'ƴa mata suna kamuwa da cututtuka masu hatsarin gaske.
  6. Talla na haddasa yawan zinace-zinace


Wadannan sune kadan daga cikin illolin da talla ke haifarwa ga rayuwar ƴaƴa mata. Yana da muhimmanci iyaye su saka ido sosai kan yaransu da suke tura su talla don gudun abinda kan iya biyo baya, Allah Ka shiriyar damu baki ɗaya.


Wallafar Babangida Ruma


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post