Illolin Dake Tattare Da Yin Amfani Da Magungunan Mata

Illolin Dake Tattare Da Yin Amfani Da Magungunan Mata
Illolin Dake Tattare Da Yin Amfani Da Magungunan Mata


Illolin Dake Tattare Da Yin Amfani Da Kayan Mata


Biyo bayan wasu ziyarce-ziyarce da muka gudanar a wasu asibitoci haɗi da yin tambayoyi kai tsaye ga wanda abin ya shafa da kuma wasu bincike da muka gudanar mun gano cewa yin amfani da kayayyakin mata na da illoli masu tasiri ga waɗanda suke yin amfani da su. 


Irin waɗannan kayan matan na iya janyo wa matan da ke amfani da su matsalolin kiwon lafiya ko zamantakewa da mazajensu.


Likitoci sun bayyana irin matsalolin da mata masu amfani da kayan mata ke fuskanta da suka haɗa da cututtuka.


Sun kuma bayyana yadda haɗin magunguna ke iya yin illa ga farjin mata, ya ɓarnata jikin nata, musamman irin wanda a ke saka shi cikin jiki.


Kaɗan daga Illolin da suke haddasawa daga yin amfani da kayan mata sun haɗa da:


1. Zubar ruwa daga al’aura

Sakamakon amfani da kayan mata na matsawa da na turare, hakan kan haifar musu da zubar ruwa mai ɗoyi daga al’aurarsu, wanda zai dinga ɓata musu dan kamfai, ka ji suna wari mai tayar da hankali. 


2. Ƙaikayin gaba:

Sakamakon amfani da kayan mata musammman ma na matsawa da na turare da wasu matan kan yi amfani dasu, sai hakan ya haifar musu da ƙaikayin gaba. 


Sukan matsa ko saka sinadarin kayan mata a al’aurarsu, ko kuma turara al’aurar tasu, wanda a ƙarshe maimakon hakan ya haifar da biyan bukata, ta hanyar samun biyan bukata, sai cibi ya zama ƙari ta hanyar samuwar ƙaikayin gaba, wanda idan suka zauna ba abin da za ka ga su na yi sai soshe-soshe.


3. Hana ɗaukar ciki

Wasu magungunan saboda ƙarfinsu sukan ɓata mahaifa ko kuma toshe inda ƙwai ke fitowa sai ka ga mace ta kasa ɗaukar ciki.


4. Ɓarin Ciki

Amfani da kayan mata yana kawo ɓarewar ciki, saboda shan maganin ake ba wani ƙa’ida ko ma’auni, kuma wasu magungunan suna da ƙarfi sosai da za su hana ciki zama a mahaifa.


5. Cutar kansa

Amfani da kayan mata barkatai yakan haifar da sanƙarar mahaifa (uterus cancer), wadda wani lokaci za ta iya kai ga macce ta rasa mahaifarta ko kuma rayuwarta gaba ɗaya.


6. Hawan jini ko saukar jini:

Sakamakon amfani da kayan mata na sha na haifar da matsalar hawan jini ko saukarsa. Kasancewar jini hanyar tafiyar da abinci, ruwan da muka sha da magungunan da muka sha.


Don haka idan kayan matan na ɗauke da wasu sinadarai masu lahani ga shi jinin ko kuma aka yawaita amfani da su, sai hakan ya kawo hauhawar jini ko saukarsa.


7. Matsanancin ciwon kai:

Kayan mata na janyo matsanancin ciwon kai ko zafin jiki. Wannan ba ya rasa nasaba da ƙarfin da maganin ya musu a jini.


8. Ciwon zuciya:

Amfani da kayan mata na haifar da ciwon zuciya, kasancewar magungunan da matan kan sha suna samun damar za ga jikinsu ne, ta hanyar zagaya sassan jiki da jini ke yi.


Haka kuma da ma zuciya ita take da haƙƙin harba jini izuwa kowane sashi na jikin ɗan Adam, sannan bayan jini ya gama zagaye jikin, yakan dawo zuwa zuciya.


Kamar yadda na yi bayani a sama, cewa kayan mata na ƙunshe da sinadarai da suke da lahani ga jini, don haka bayan jini ya kwashi waɗannan sinadarai, ya zaga jiki da su, sannan ya dawo zuwa zuciya, hakan sai ta sanya taruwar waɗannan sinadarai a zuciya, inda a nan sai ka samu sun haifar da ciwon zuciya, idan ma an samu kumburar fatar da take ba da kariya ga zuciya ko kuma haifar da naƙasu ga ita zuciyar wajen harba jini zuwa ga sassan jiki.


Ta ɓangaren mu’amala da zamantakewa kuma, mata kan fuskanci matsaloli kamar haka:


1. Cire wa miji sha’awar matarsa

Da zarar magunguna da aka yi wa mace kafin ta shiga gidan mijinta ya gushe, to ni’imarta za ta ragu da kashi 80% sai ta asali da take da ita ta dawo.


Shi kuma miji ba zai dinga jin tana gamsar da shi kamar da ba. Daganan sha’awa da yake mata za ta fara raguwa, idan aka yi rashin sa’a sai ma ya haifar masa da sha’awar wasu matan a waje.


2. Gusar da ni’imar mace ta asali da take da ita:

Duk macen duniya, akwai ni’imar da Allah Yai mata wajen gamsar da namiji, amma irin ni’imar kayan mata na iya haifar masu da illa wajen gusar da ni’imar da suke da ita ta asali. Domin da zarar aikin waɗannan magungunan ya gushe, to ni’imarta ta asali da take da ita ma za ta ragu.


3. Rashin tattali da tanadi:

Mata da yawa da suka saba siyan kayan ba su da tanadi ko tattali, don a kullum tunaninsu yadda za su samu kuɗin sayan kayan matan ne.


Daga Samira Bello Shinko.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post