Idan Kina Son Namiji Yayi Kewar ki, Ki Yi Masa Waɗannan Abubuwan |
Suma mata yana da kyau su yi amfani da dabarun da zasu riƙa saka samarinsu dake son su da aure kewa. Ba wai kawai shi namiji ne kaɗai zai cusa miki kaunarsa ke kuma baki da hanyar saka shi ya so ki. Don haka idan baki san yadda zaki da namiji ya so ki ba ga wasu dabarun da duk budurwa za ta riƙa sa mai son ta da kewarta.
Idan kina son namiji ya riƙa kewarki kada ki zamemasa mace mai arha. A duk lokacin da yake son ganinki ya ganki. Dole ne ki riƙa taƙaita yawan baiwa mai sonki lokaci domin rashin samun lokacinki a yadda yake so ne zai sa kiyi daraja a wurinsa kuma ya riƙa ɗoki da kewarki.
Wasu lokacin ki nuna masa ayyuka ne na gida a gabanki koda kuwa baki aikin komai. Wani lokacin kuma ki nuna masa baza a barki ki fito ba. Wasu lokutan kuma nuna masa karatu kike tare da bashi haƙuri da sabon lokacin da za ku sake haɗuwa.
Duk lokacin da kuka haɗu da mai sonki ki tabbatar masa babu namijinki da kike so a duniya sai shi. Ki nuna masa idan dai maganar soyaya ne babu wani namiji da yake so sai shi. Hakan zai riƙa tabbatar masa da cewa baki taƙaita kanki a wajensa bane saboda bakison shi.
Idan kina son ki riƙa sa mai sonki kewa da kuma ganin sa da daraja ki taƙaita yawan ɗaukan wayarsa, yi masa reply a lokacin da yake so. Da kuma doguwar hira da shi a waya.
Idan saurayinki ya kiraki to ki ɗan bada lokaci kafin ki kira shi ko sai ya sake kiranki sannan ki ɗauka.
Haka kuma ko saƙo ya turo miki manta da saƙon zuwa wani ɗan lokaci kafin ki bashi amsa cikin girmamawa da kuma mutuntawa.
Haka idan ya kira waya kada ki bari ya jaki da hira har sai zancen da yake son yi miki ya gama. Bar shi sai ya gangaro a bayanin nasa sai kice masa yayi haƙuri zaku ci gaba da maganar koda kuwa maganar da yake miki tana miki daɗin ji fiye da shi mai baki labarin.
Idan kin tashi kiran saurayinki a waya kada ki bar shi ya fahimci wani lokaci na musamman da kike kiranshi. Ya zamanto a kowani lokaci kina iya kiranshi a lokacin da baya zato. Kuma kada ya zama kina kiransa fiye da sau ɗaya a rana, wata ranar ma shareshi kawai kamar kin manta da shi.
Idan kika tashi tura masa saƙon text kada ki riƙa tura masa doguwan hira ko labari. Yi masa gaisuwa ko bayani a taƙaice yadda zai so ya samu ƙarin bayani. Muddin zaki kula da waɗannan dabarun, zaki yi mutunci a wajen mai son ki da aure, kuma a kullum zai riƙa kewarki.
Idan kina son namiji yayi kewarki ki samu wani lokaci kina likes na post dinsa ko yin koment. Wani lokacin ma ki tura masa saƙo a inbox dinsa musamman idan yayi abinda ya burgeki. Can kuma kawai sai ki ɗauke wuta duk abunda zai yi posting ko zai faɗa kama tagging zai miki kada ki ce komai kaman baki gani ba.
Wannan yakan jawowa mace ƙima da cusawa namiji ƙoƙarin ganin kada ta kuɓuce. Don haka a kullum zai yita kewarta. Wani lokacin dif zaki yiwa saurayinki ya kasa samun ki a waya ko kuma ganinki.
Ita mace tana ƙara daraja ne a wajen namiji gwargwadon ƙarancin da take masa. Idan mace ta zama available a wajen namiji ba zata yi darajar da ya kamata tayi ba. Sai dai wannan ba yana nufin cewa mace zata ƙauracewa mai sonta bane har yadda zai ga tamkar bata son sa ne.
A zahiri da kuma baɗini ya tabbatar kina sonsa. Amma ki zama baki bada kanki arha yadda zai ji tamkar shi yake da iko dake kamar matarsa. Dole ne ki riƙa cusa masa shakku a ransa na kina sonsa ne ko baki sonsa. Tare kuma da nuna masa cewa har yanzu fa yana da sauran aiki a gabansa muddin yana so ya riƙa ganinki yadda yake so a lokacin da yake so.
A kewa, shi namiji yana ƙokarin ƙara kusanci da mace ne. Ita kuma mace idan tana son namiji yayi kewar ta zata riƙa masa rowan kanta ne. A haka sai kuka kowa yana ɗokin kowa, kowa yana marmarin ayi aure. Da fatan samari da ƴan mata sun fahimci wannan karatun.