Hirar Kalaman So Tsakanin Saurayi Da Budurwa |
Nakan ji ba dadi a rayuwata a duk lokacin da nayi nisa dake, sannan babu wani abinda ke zame min mai wahala irin kwatancen yadda nake so da kaunarki a rayuwata.
Hirar kalaman soyayya a tsakanin saurayi da budurwa yana kara fadada soyayya da kaunar juna. Idan masoya sun san kalaman soyayya masu rasta zukatan su tabbatas za samu Karin dankon soyayya dake tsakanin su.
- Saurayi: rabin raina ya kike?
- Budurwa: qalau nake abin alfahari na?
- Saurayi: da fatan babu wata matsala ko damuwa dake a tare dake Koh?
- Budurwa: hmmm, matsala daya ce..... Kana sona sosai, kuma ya kake ji idan bamu tare?
- Saurayi: nakan ji ba dadi a rayuwata a duk lokacin da nayi nisa dake, sannan babu wani abinda ke zame min mai wahala irin kwatancen yadda nake so da kaunarki a rayuwata.
- Budurwa: nasan da haka abin alfaharina.... Ko zaka iya kasancewa dani har abada a matsayin abokiyar rayuwarka?
- Saurayi: baza ki taba ganewa ba, kasancewa dake shine rayuwa a gareni.... So da kaunarki ke tafiyar da rayuwa ta ciki farin ciki da nishadi. Rashin haka kuma zai zame min kunci da tsanani a rayuwata mara yankewa har abada.
Menene Ra'ayin Ku Game Da Kalaman Da Saurayin nan Ke Zubar Ma Budurwarsa.. Ku bayyana mana ra'ayoyin ku a kasan wannan rubutun.