Hanyoyin Ingantattu Na Gyaran Nono |
Hanyoyin Gyaran Nono Don Matan Aure Da 'Yan Mata
Matan dake son su rage girman nono da matan dake son su Ƙara girman nono yau na zo muku da wasu hanyoyi yadda za ku magance waɗannan matsalar.
Hanyoyin Rage Girman Nono
Ina matan dake ƙorafin rage girman nonon su, ga wata hanya da na zo muku da ita mafi sauƙi da za ku yi amfani da ita don rage girman nono. Za ku samu waɗannan abubuwan kamar haka;
Ganyen lemun zaki Buhuru Sudan iya. Ki haɗa ki dakasu ki dinga shafawa a nonon, duk girman nono ki zai ragu. Amma ki rage shan madara Ki dinga soya hanta da kitsen akuya kina ci za su ragu.
Hanyoyin Magance Saurin Kwanciyar Nono
Kina budurwa kinaso kada nononki ya zube, kafin aurenki ki daina saka ɗamanmu kaya, kuma babu bra, ko ki rinƙa tsalle da sauransu kuma ki daina kwanciya rub da ciki ko ki rinƙa ɗaga zani sama kina ɗamesu. Kuma rashin shan kayan marmari da rashin saka bra suma suna kawo saurin zubewar nono.
Hanyar Yadda Za Ki Yi Gyaran Nono
Za ki samu waɗannan abubuwan kamar haka;
1) Alkama
2) Madara
Zaki yi shi sau biyu a rana zaki yi hakan kafin sati biyu a yi iyaye da kuma sati biyu bayan iyaye.
Sannan za ki samu Hulba a tafasa ki rinƙa gasa nono da shi. Sai kuma a shafa man hulba za'a ga abin mamaki. Sannan za ki samu waɗannan abubuwan kamar haka;
1) Ganyen tatarida
2) Wake
3) Gujjiya
4) Alkama
Ki samu wake kamar gwangwani ɗaya, gujjiya gwangwani biyu, alkama gwangwani biyu, ki kai inji a niƙa miki, ki daka ganyen tatarida gari gwangwani ɗaya ki haɗa guri guda ki dinga zubawa a nono kindirmo mara tsami kina sha amma garin magani cokali biyu.
Yadda Za Ki Yi Idan Kina Son Cikowar Nono
Idan kina son cikowar nono, za ki samu waɗannan abubuwan kamar haka;
1) Habbatus sauda
2) Hulba
3) Shinkafa
4) Madara
Zaki haɗe su guri ɗaya, sai ki riƙa yin kunu kina sha kafin awa biyu da yin barci sannan awa biyu bayan breakfast, ki hanzarta yin wannan haɗin, da izinin Allah za'a ga biyan buƙata.