Hanyoyi 15 Da Namiji Zai Saka Matarsa Cikin Farin Ciki

Hanyoyi 15 Da Namiji Zai Saka Matarsa Cikin Farin Ciki
Hanyoyi 15 Da Namiji Zai Saka Matarsa Cikin Farin Ciki 


Hanyoyi 15 Da Namiji Zai Saka Matarsa Cikin Farin Ciki 


Da yawa daga cikin maza basu san hanyoyin da ake amfani dasu domin nuna soyayya da saka farin ciki a zukatan matansu ba. Hakan yasa a wannan topic na yau muka tattaro muku wasu daga cikin hanyoyin da za'a saka mata cikin farin ciki da kara tabbatar da zaman aure, kuna iya latsa wannan shudin rubutun ku kalli VIDEO kan cikakken bayani. Ga su kamar haka;


1- Idan ka dawo ka shiga gidan kace Assalamualaikum' sha'aidan zai bar gidan!.


2- Ka rika yawan bata labarai. Saboda Allah (S.w.t) ya sanar da mu dan Adam yana son labari.


3- Ka zama mai yawan yabonta, musamman a wajen da ake kusheta ka nuna ɓacin ranka.


4- Ka zama mai yawan bata kyaututtuka. Kyauta tana ƙara dankon soyayya.


5- Ka share wasu daga cikin kuskurenta. Ka nuna baka ma san ta yi ba. Kuma ka ɗauka a matsayin abinda ya shuɗe, karka ajiye shi a kwakwalwarka.


6- Ka nuna mata tausayawarka gareta a fili, musamman a lokacin da take da juna biyu ko take jinin al'ada.


7- Kada ka ɗaukaka abokanka fiye da matarka. (lokuta da dama wasu mazan suna fifita abokansu na karatu ko na sana,a sama da matansu).


8- Ka nuna mata babu wata budurwa dake gabanka sai ita, Ka nuna mata kullum a matsayin sabuwa take a gurinka.


9- Ka riƙa tunawa da ita a cikin addu'arka. Hakan zai ƙara kauna tsakaninku.


10- Kada ka nuna mata ce wa kana yi mata alfarma akan wani kyauta da kake mata, kamar siyan abinci,Saboda daman hakkinta ne ka kawo mata, sannan kasan ce wa abincin kawai kake kawowa amma Allah shi ne mai ciyarwa.


11- Shaiɗan ne abokin gabarka ba matarka ba. Lokuta da dama idan mata da miji suka ɗan samu saɓani har takai ana maida martani cikin fushi,To katuna ba daga ita bane shaiɗan ne ke zugata, Saboda shi yana mutuƙar son ayi saki.


12- Ka ɗauki abinci ka saka mata abaki. Annabi (s.a.w) ya ce, "abincin ba cikinta kaɗai zai shiga ba, zai huce har zuwa zuciyarta."


13- Ka kasance mai yawan yi mata murmushi/fara'a domin Manzo (s.a.w) ya ce: "Duk wanda ya nunawa matarsa fara'arsa to dai-dai yake da yin sadaka."


14- Ka zama mai yawan neman shawararta. (wasu suna ce wa ba'a shawara da mata). To ku sani ce wa manzo (s.a.w) ya kasance yana shawara da matansa.


15- Kar ka ɓoye mata damuwar ka, farin cikinka ko bakin cikinka. Domin ita magani ce a tattare dakai.


Waɗannan sune hanyoyi 15 da suka dace maza su dinga yiwa matansu domin hakan yana saka su farin ciki idan an nuna ana ƙaunar su.


Kuna iya latsa nan don kallon cikakken bayani kan yadda Namiji Zai saka matarsa farin ciki. 

VIDEO 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

1 Comments

  1. Sukuma matan babu hanyoyin da zasu farantawa maxan domin kara donkon soyayyar ko

    ReplyDelete
Previous Post Next Post