Halin Da Mutum Zai Iya shiga Idan Ya Dauki Lokaci Ba Tare Da Jima'i Ba |
Halin Da Mutum Zai Iya shiga Idan Ya Dauki Lokaci Ba Tare Da Jima'i Ba
Ga wanda dama can bai tabayi ba, yanada sauki kamunwa da hadarin rashin yin Jima'i. Amma ga duk namijin da ya saba kuma ya jima bai yi ba, hakan na iya haddasa masa matsaloli a lafiyar sa kamar yadda za ku ji cikakken bayani idan kun Kalli wannan VIDEO
Ga wasu illolin da mazan da suka jima ba su yi Jima'i suke fuskanta akan lafiyarsu.
1:Matsalar Saurin Inzali: Kamar yadda mukayi bayani a baya, rashin sabo da da Jima'i na jawo saurin zuwan kai, haka nan yawan Jima'i na magance saurin zuwan kai.
Ga duk namijin daya jima baiyi Jima'i ba zai samu matsalar Saurin Inzali a duk lokacin da ya tashi yin Jima'i.
2: Ciwon Maraina: Akwai wani cuta da likitoci suke kira prostate cancer. Wannan cutar yana shafar mafitsaran namiji ne da kuma haddasa masa cutar gwaiwa.
Binciken masana ya gano duk namijin da zai yi zuwan kai akalla sau 21 a duk wata, bazai kamu da irin wannan cutar na mafitsara ko na gwaiwa ba kamar yadda za ku ji a wannan VIDEO. Duk namijin da baya samun yin yadda ya kamata, akwai yiwuwar kamuwa da wannan cutar inji masana.
3: Ciwon Hawan Jini: Rashin samun yin Jima'i yadda ya kamata ga namiji na iya haddasa masa cutar hawan jini. Idan kuma daman yanada shi zai kara ruruta cutar. Ganin yadda gudanar da Jima'i nasa mutum jininsa ya zagaye jikinsa yadda ya kamata. Haka rashin Jima'i nasa jinin mutum yayi sanyin da zai iya haifar masa da cutar hawan jini.
4: Yana Nakasa Garkuwa Jiki: Daukan lokaci mai tsawo ba tare da tarawa da iyali ba yakan ragewa sinadarin kariya na jikin mutum su yi rauni, yadda kamar cuta tana iya addaban namiji idan ta kamashi. Amma duk namijin da yake yi akai akai duk cutar da ta tinkaroshi bugu guda yake mata ta mace.
5: Ciwon Gabobi: Duk namijin da bai samun yin Jima'i yadda ya kamata a cikin kasala yake a kullum. Yawan gudanar da Jima'i ga maza na saka su kasancewa cikin kuzari karfin jiki.
Wadannan sune wasu daga cikin illolin rashin samun gudanar da Jima'i ga duk wani namiji. Don haka ga magidanta Maza ba abun burgewa bane su rika kin Jima'i da matansu akai akai ba. Ku kalli wannan VIDEO don jin cikakken bayani kan halin da ake samun kai idan ba'a yin Jima'i
A darasi na gaba suma mata za su ci illar da rashin gudanar da Jima'i akai akai ga mazajensu.
Ba muce mara aure yaje ya kama zina ba saboda ya samu lafiyar da Jima'i yake samar wa. Magane da maza masu aure da suke kaucewa yin Jima'i akai akai da su muke magana.