Halayen Matan Social Media |
Halayen Matan Social Media
Shin kunsan irin halayyar yan matan social media kuwa? Idan baku sani ba ku Karanta wannan takaitaccen bayanin kamar haka.
Ƴan mata suna complain akan samarinsu basa kulawa dasu, to su samari ai ba mahaukata bane. Idan kaji mace tace saurayinta yana kulawa da ita nufin ta fa saurayin da zai sa ta a gaba yayi ta kashe mata kudade yana yi mata dawainiya kamar bai san zafin kudaden ba ko kuma ba wahala yake yi ya samu ba.
Mace idan kace mata kwana biyu bana ganinki online sai kayi sa'a ne ma zata ce maka data ne matsalanta wata sai kaga tana neman daura maka nauyin siya mata waya.
Wata zaka ce mata tachi abinchi kuwa kawai sai ta fara maganar ka siya mata kaza ko shawarma wata zatayi status kamar tana cikin damuwa kana yi mata reply zata fara maka maganar bata da kudi.
Gaba daya in kasan baka da kudi to kar ma ka fara cewa zaka wani bawa mace kulawa wlh ko kiranta ka fiyeyi don kaji yadda take kafin ta daga wata sai ta fara zaginka tace wannan ya cika takura.
Kulawa a wajen wasu matan ka tanadi kudi kawai daga sun dan yi motsi ko yaya ne ka jikasu da kudi amma duk wani kiran wayarka da wani zuwa zanchenka da wani yi mata text duk na banza ne.
KABIR
ReplyDelete