Halayen Mace Tagari Da Yadda Ake Gane Su Cikin Mata

Halayen Mace Tagari Da Yadda Ake Gane Su Cikin Mata
Siffofin Mace Tagari 


A Zamantakewar Soyayya: Shin Wace Ce Mace Tagari?


Masu salon Magana suna cewa, kowa yana son mace mai kyau, sai dai idan bai samu ba. Burin kowane namiji shi ne ya samu mace ta gari. Sai dai ga dukkan alamu wasu basu san ma wace ce mace ta gari ba. Idan ba ka san yanayi da halayen mace tagari ba, saurari abinda MUSA B MALAM zai fada maka


Mace tagari, ita ce wacce ta mallaki waɗannan halaye guda goma sha ɗaya, kamar haka:


1- Mace ta gari itace Idan mijinta ya kalle ta zai ji farin ciki ya lullube shi.


2-Ita ce wacce take gaggawa wajen cika umurnin mijinta.


3- Mata tagari, ita ce wacce take matuƙar kiyaye duk abin da zai ɓata wa mijinta rai. 


4-Ita ce wacce take dagewa wajen bautar Ubangijinta.


5- Mata tagari ita ce wacce ba ta yin wasa da duk wani haƙƙi na mijinta.


6-Ita ce wacce duk lokacin da mijinta ya yi fushi, ba ta samun kwanciyar hankali har sai ta yardar da shi.


7- Mace ta gari,bIta ce wacce take kiyaye duk wani sirrin mijinta.


8-Ita ce wacce idan mijinta ba ya nan take kiyaye mutuncin kanta, da kuma dukiyar da ya bari a gida.


9-Ita ce wacce take kulawa da tarbiyyar mijinta da ’ya’yansa ko da ba ita ce ta haife su ba.


10-Ita ce wacce take matukar girmama iyayen mijinta, kamar yadda take girmama nata iyayen kuma take kyautata wa ’yan uwansa ba tare da tsangwama ba.


11- Mata ta gari Ita ce wacce take zama da maƙwabtan ta da kishiyoyinta cikin tsoron Allah da kyautatawa, ko da su suna munana mata.


Garin daɗi na nesa wai angulu ta leƙa masai, Duk macen da ta mallaki waɗannan halaye, babu shakka ta mallaki halayen ’yan Aljanna. Allah Ka sanya mu kasance nagari a halayya da ɗabi’a, mazanmu da matanmu, Amin.


Siffofin Mace Ta Gari 

Mace tagari itace wacce zata auri mutum ba don wani abu da yake dashi ba na kuɗi, ko mulki, ko wata burga ta duniya masu gushewa. A'a sai don addininsa da amanarsa kawai wanda zai sa su yi rayuwa a duniya cikin jin daɗi, su mutu su samu aljannar ubangiji saboda sun so juna don Allah, sun yi aure akan ɗa'ar Allah sannan sun yi zama irin wanda Allah yayi umarni da a yi tsakanin ma'aurata a musulunci. 


Ga Wasu Daga Cikin Siffofin Mace Tagari

1 kiyaye lokutan ibada

2 kiyaye sirrin miji

3 juriya da haƙuri

4 wanka da ado

5 gyaran jiki

6 kwantarwa da miji hankali

7 kiyaye lokotan jima'i

8 gudun zargi

9 taimakawa miji

10 danne fushi

11 tarbiyantar da ƴaƴa

12 dauwama kan neman ilimin addini bisa yardar miji.


Mace tagari bata aikata kishiyoyin abinda ambatonsu ya gabata. Haka zalika mace tagari bata aikata waɗannan abubuwan kamar haka 


1 bata ɗaukaka sautinta akan mijinta.

2 bata satar kayan abinci ko kuɗin miji.

3 bata saka sharaɗi idan miji yazo zai tara da ita.


Mace tagari itace wadda a duk lokacin da miji ya kalleta zaiji farin ciki ya lullubeshi, so da ƙaunarta ya ƙara ƙaruwa a cikin masarautar zuciyarsa. 


Ya Allah ka haɗamu da irin waɗannan mata idan akwaisu a duniya albarkacin manzon tsira Annabi Muhammad (SAW), Amin.

 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post