Yadda Zaki Matse Gabanki |
Matse Gabanki: Ana dafa bagaruwa da ganyen magarya ki rika wanke gabanki dashi kina zauna a ciki da dumi kamar minti 30, a kalla sau biyu a sati.
Ana so ko da yaushe idan mijinki zai kusance ki yaji ki gabanki a matse yake, don ba'a son lokacin da miji zai yi jima’i da matarsa ya wuce siririf babu wani alamun masti. Don haka yana da kyau duk mace musamman wacce ke da aure ta rika kula da gabanta kar ya bude.
Kafin mu bayyana miki yadda za ki matse gabanki yana da muhimmanci ki san abubuwan dake jawo budewar gabanki. Ga su kamar haka;
- Haihuwa; Babban abinda ke jawo gaban mace ya bude shine haihuwa.
- Istimna'i; shine mace ta dinga biyawa kanta bukata don taji dadi ta hanyar yin amfani da wani cikin gabanta.
- Saduwa; Yin Jima'i yau da gobe idan mace bata kula da gabanta zai bude.
Wannan kadan ne daga cikin wadannan dake jawo budewar gaban mace, domin ba za mu iya kawo muku su duka ba.
Yadda Za Ki Matse Gabanki
Akwai hanyoyi na yadda za ki matse gabanki domin suna da yawa, ga wasu daga cikin su:
- Bagaruwan: Ana dafa ta da ganyen magarya ko ita kadai ki rika wanke gabanki dashi ko ki zuba a baho ki zauna a ciki da dumi kamar minti 30, a kalla sau biyu a sati.
- Kanunfari: Ana dafa shi a sha da zuma da zafi zafi, ko ki jika ya kwana da safe ki tace kisha da madara da zuma. Ana kuma dafa ta a zauna a ciki da dumin ta ko a rika tsarki da ruwan ko kuma a zuba kanunfari kan garwashi a tsugunna, shi ma sau 2 a sati.
- Kwallon Mangwaro: Idan kika fasa zaki ga dan cikn fari ne, ana busar dashi a daka a kwaba da zuma a rika matsi da shi bayan isha’i. Idan zaki kwanta bacci ki wanke ko kuma ki dafa dan cikin da bagaruwa ki wuni tsarki dashi ko ki zauna a ciki, shima a kalla sau 3 a sati.
- Almiski: ki samu fari ko ja ki daka kanunfari ki tankade yai laushi sai ki kwaba da miskin da man zaitun. Yawaita amfani dashi na matse mace sosai kuma kullum cikin kashi gabanki zai kasance. Yana gyara macen da ta haihu sosai musamman da jinin haihuwa ya dauke ki fara amfani dashi har kiyi kwana ar’bain. Idan wannan ta faru dake Zaki iya tsarki da; Ruwan dumi da Bagaruwa
Na tsawon Wata guda, sai kuma matsi shi kuma za ki yi shi saura sati biyu aurenki kuma wannan mun dade da yin bayaninsa.
Yadda Za Ki Hadin Matse Gabanki
- Ki daka garin zogale ki tankadeshi.
- Ki samu man kadanya (Ana samu a wajen masu maganin gargajiya.
- Ki samu man zogale (Ana samu a wajen masu Islamic-medical-centre.)
- Ki samu Karo, shine wanda ake tawada dashi kuma ana wanke hula dashi (Ana samun sa wajen masu kayan koli).
Ki samu man shanu (ana samunsa a wajen masu sayar da nono). Duk ki hada su guri daya, ki kwaba su suyi kamar sa’oi 5, za kiga sun hade, sai Kiyi Matsi dashi. kuma Zaki iya rabashi 3 Kiyi matsi dashi Sau uku a cikin sati biyu.