Don Masu Aure: Abubuwa 5 da ya kamata ku yi bankwana da su bayan kun yi aure

Don Masu Aure: Abubuwa 5 da ya kamata ku yi bankwana da su bayan kun yi aure
Abubuwa 5 da ya kamata ku yi bankwana da su bayan kun yi aure


Don Masu Aure: Abubuwa 5 da ya kamata ku yi bankwana da su bayan kun yi aure


Aure abu ne mai ban sha'awa, amma yana da iyaka. Ɗaya daga cikin manyan abubuwa game da rashin aure, shine za ka dinga yin wasu abubuwa na rashin dacewa, sai dai wasu bayan sun yi aure suna yin kewar abubuwan da suka saba yi kafin su yi aure. 


A Wannan rubutu Mun kawo muku abubuwa guda 5 da ya kamata ku yi bankwana da su bayan kun yi aure. Kuna iya kallon wannan video domin jin cikakken bayani. 


Abubuwa 5 da ya kamata ku yi bankwana da su bayan kun yi aure

Ga jerin abubuwa biyar da ya zama wajibi ku Kauracewa aikatawa idan kun yi aure gasu kamar haka;


(1) Kada dayanku ya Kasancewa mai son kai

Aure tsakanin mutane biyu ne. Babban muhimmin abin da yawancin ku ke rasawa shine 'daidaitawa'. Aure yana nufin kasancewa daya. Idan Kana ko kina yin wasu abubuwa don kanka ko kuma don kanki kafin aure to yana da kyau ku sani cewa yanzu ku ma'aurata ne babu magnar nuna son rai. Yanar da kyau ku samu daidaito a tsakanin ku. Ku yiwa junanku adalci. 


(2) Yin bacci A Wani Waje ba gidan auren ku ba

Barin gidan auren ku don yin bacci a wurin abokanku dole ne a dakatar da shi. Sai dai Idan ya kama, misali Idan ka yi tafiya zuwa wani garin ko wani abu makaman cin haka. 


(3) Karbar shawararin aure daga abokai marasa aure

Daukar shawarwari daga wajen abokanai musamman wadanda ba su yi aure ba yana daya daga cikin abubuwan da ya kamata ku kaucewa, domin shawarwarin aure sai wanda yai auren shine yasan irin matsalolin da ake fuskanta. Abokai marasa aure ba su da wani tunanin yadda rayuwar aure take. Don haka idan ka yi aure ka guji neman shawarwari daga wajen abokanan ka wanda ba su yi auren ba. 


(4) Yin tarayya da wasu matan na daban

Idan Kana yin tarayya da wasu matan yana da muhimmanci ka watsar a yayin da ka yi aure, domin wasu mazan ko da sun yi aure basa daina dab'iar yin muamala da wasu matan. Wasu kuwa basa daina yin wannan dab'iar ta zuwa gidan cin abinci da kawayen su mata, ku sani Idan kun yi aure babu wacce tafi cancanta kuje gidan cin abinci ko wajen shakatawa sai matan ku. 


(5) Sanya hotuna masu tayar da hankali a shafukan sada zumunta

Sanya hotunan tsirara a kafafen sada zumunta na yanar gizo ya zama ruwan dare ga maza da mata a wannan zamanin, irin wannan yafi faruwa ga mata, kuma ko bayan sun yi aure za ka samu suna dora hotunan su a social midiya wasu mazan na daban suna gani. Kisani Idan kin yi aure kidaina tura hotunan ki wasu mazan na daban suna kallon ki.


Wadannan sune jerin abubuwa 5 da yakamata ku yi bankwana dasu idan kunyi aure da fatan ma'aurata za su kiyaye hakkin junansu da kare mutuncinsu. Kuna iya kallon wannan video domin jin cikakken bayani kan abubuwan da ya kamata ma'aurata su Kauracewa yi idan sun yi aure.

Video 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post