Yadda Ake Tinkari Budurwar Da Kuka Hadu A Hanya |
Hanyoyin Yadda Ake Tinkari Budurwar Da Kuka Hadu A Hanya A Karon Farko
Ba duka samari ne suka san yadda ake tinkarar budurwa a haduwar farko ba. Yawanci maza da dama suna tare da matan da suka aura ne bayan haduwarsu a hanya. Soyayya babu yadda bata iya kasancewa. Sannan sanadin aure yana da hanyoyi da dama.
Maza da dama sukan haɗu da matan da suke so a hanya, amma basu san yadda ake tinkarar su ba don yi musu magana saboda rashin sanin abinda zai biyo baya. Wasu kuwa idan sunyi magana maimakon su dace sai anyi banza dasu ko abun ya zama fada.
Yadda Ake Tinkari Budurwar A Hanya Don A Bayyana Mata So
Idan kana son ka yiwa budurwa magana abu ne mai sauƙi idan har kasan abubuwan da za ka furta mata da zai jawo hanalkinta. Ga yadda zaka tinkari kan duk wata macen da ka gani a hanya kuma kaji kana sonta.
1: Da zaran ka haɗu da macen da ta yi maka a kan hanyarta na zuwa wani waje. Kafin ka yi mata magana ka tabbatar da cewa a halin da take ciki zata iya baka lakaci. Akwai matan da suke fitowa yawo ne kawai na ganin gari. Akwai masu unzuri ( makaranta ko unguwa). Akwai kuma masu uzurin da ba zai hanasu sauraron mutum ba musamman idan yayi musu magana.
Da yake kai bazaka iya fahimtarta ba. Abun lura anan shine yanayin ta da halin da take ciki a wannan lokacin zai fadamaka uzurinta na gaggawa na ko wanda zata iya sauraronka ne ko akasin hakan.
1: Yadda ake tinkarar budurwa shine, Kayi ƙoƙarin haɗa idanuwa da ita, ka haɗa kuma da murmushi tun daga nesa kafin nan ku haɗu. Wannan alamu ne da zasu sanar da ita mai wannan murmushin fa akwai magana a bakinsa.
Munsha sanarwa maza kada ka nunawa mace izza a lokacin da kake neman hanyar shawo kanta. Ka kasance namiji mai sauƙin kai duk irin matsayinka a gabanta. Ta haka ne kawai zata baka lokaci. Don haka nunawa mace wasu alamu na jiki kafin ma ka yi mata magana a haɗuwarku alamu ne da zata gane sonta kake.
2: Akwai mazan da idan suna son magana da macen a farkon haɗuwarsu kuma ba su san sunansu ba. Sai su soma cewa, "Ina magana, baki ji ba, dake nake fa, ke , siiiii". Wannan ya nuna baka san yadda ake tinkarar mace ba. Duk wata mace mai mutunci bazata taɓa sauraronka ba. Idan ma ta tsaya baƙar magana zata yi maka. Hanya mafi sauƙi idan baka san sunanta ba yi mata sallama. Wannan shine yadda ya dace kayi ga duk wata macen daka haɗu da ita a farkon haɗuwa.
3: Kada ka tinkari mace da tsoro ko sanyin jiki. Da zaran ta amsa sallamar ka ƙarasa wajenta da nuna mazantakar ka, haka mata suke so. Ka isa gabanta da wata kalmar da zai kambamata ko ya saka ta dariya. Da wannan ne zaka cusa kanka cikinta.
4: Kafin ka furta abunda yasa ka tsaida ita nemi izzininta na sanin ko tana da lokacin sauraronka saboda saƙon dake gareka zuwa gareta. Amsar da ta baka musamman idan tana sauri kada ka nemi dole sai ta saurareka. Bata dama, nemi yadda zaka iya ganinta. Idan har ta faɗamaka gidansu ko ta baka lambar wayar ta. Hakan ya nuna tana ra'ayinka ne.
5: Idan ta baka lokaci kada Kai tsaye ka soma cewa sonta kake har sai ka fadamata wasu abubuwa muhimmai da suka jawo hankalinka a gareta kafin nan ka fadamata soyayyar ka.
Cewa mace kai tsaye yanzu ka ganta kana sonta ba tare da wani dalili ba zata tunanin kawai sha'awar ta kake.
Wadannan sune hanyoyin yadda ake tinkarar budurwa a haɗuwar farko.Da fatan maza musamman samari za su yi amfani da wannan dabarun. Kuma da fatan har idan ba son mace dagaske kake ba kada ka tinkareta.