Domin Masu Aure: Yadda Ake Yin Haɗin Ƙarin Ni'ima Da Gyada Da Namijin Goro
Domin Ma'aurata: Yadda Ake Yin Hadin Karin Ni'ima Da Gyada Da Namijin Goro |
Yadda Ake Yin Hadin Karin Ni'ima Da Gyada Da Namijin Goro: Wannan Hadin Yana Taimakawa Ma'aurata
Da yawa daga cikin ma'aurata akwai waɗanda basa iya kusantar iyalinsu ba tare da sun sha magani ba, wani kuma da zarar ya kusanci iyalinsa sau 1 baya iya sake maimaitawa sai kuma tsawon wani lokacin saboda domin ya riga da ya yi inzali wanda kuma sai ya ɗauki wani lokaci kafin ya sake jin wata sha'awa.
Wasu ma'auratan suna yin amfani da magunguna irin na chemist domin su Ƙara ƙarfin kuzarinsu, wanda bai fiya yin tasiri a jiki ba, idan ma yayi aiki ba zai wuce lokacin da ka sha ba.
Wasu matan suna yin amfani da abubuwa su saka a gabansu da nufin ya ƙara musu ni'ima da sha'awa a yayin Jima'i. Idan kina ko kana daga cikin masu irin waɗannan matsalolin da muka ambata ga wani haɗi da nazo muku dashi.
Yadda Ake Yin Haɗin
Wannan wani haɗin magani ne da nazo muku dashi wanda idan kun yi amfani dashi ba za ku ƙara neman wani maganin neman Ƙarin Kuzari ko Ƙarin sha'awa ba. Ku nemi waɗannan abubuwa kamar haka;
- Namijin Goro (biter kola) 10
- Gyada
- Madara
Ana so a samu busahshen namiji goro, sai a haɗa da gyada a niƙa, za ku dinga ɗiba a ƙaramin cokali ana zubawa cikin madara. Da yamma za ki sha, shima Mijinki ya sha. Kuna iya kallon wannan video don ganin yadda ake yin haɗin.
Duk Wata ƙwayar cuta dake jikin marar namiji ko mace, za ku yi fitsarin wannan cutar dake jikin ku. Sannan zai ƙarawa namiji ƙarfi da Kuzari A duk lokacin da yake son yin Jima'i.
Matan dake da matsalar bushewar gaba, daukewar sha'awa, rashin ni'ima idan kuna yin amfani da wannan hadin za ku samu lafiya da ni'ima.
Ku latsa nan domin kallon video yadda ake yin haɗin.
Leave Comments
Post a Comment