Domin Masoya: Saƙon Soyayya Na Safe

Domin Masoya: Saƙon Soyayya Na Safe
Saƙon Soyayya Na Safe


A wannan topic za ku koyi Zafafan Saƙonni Soyayya na barka da safiya masu ratsa zukatan masoya


Akwai kalaman soyayya masu ratsa jiki da zuciya da ya dace masoya su dinga yin amfani dasu musamman irin sakon soyayya na barka da safiya da suke ƙara soyayyar juna. Ga saƙonnin soyayya na barka da safiya kamar haka;


Idan Babu Ke Rayuwa Zata Yi Min Kunci

A dukkan lokacin da na rasa ki, zan rayu ne cikin ƙunci da damuwa, hakan ya sanya a kullum nake cewa, idan babu ke ba zan iya rayuwa ba, karda ki gwada ni a kan haka dan Allah, domin kuwa yin hakan ka iya tarwatsa farin cikina, Ina Son Ki masoya.


Kina Da Kwarjini 

A dukkan lokacin da na hango ki sai nake jin fargaba da tsoron tinkarar ki, saboda kwarjininki, hakan ke sanya wa na gaza furta miki cewa Ina Son Ki, duk da dai har yanzu na gaza bayyana miki fuskata, amma ina son fara ganin saƙon amincewarki ga tayin soyayyar tawa kafın faruwar hakan. Na san kin sha ganin saƙonnina, zan kuma ci-gaba da baki kulawa, domin samun farin cikinki. Ki huta lafiya. Ina Son Ki.


Ruhinmu Ya Zamo Guda Daya 

SO ka iya haɗa ruhi da ruhi su rayu a jikin gangar jiki guda ɗaya, kamar yadda ya hada nawa da naki. Tabbas a dukkan yanayin da kike ciki na farin ciki ko damuwa, nima na kan kasance cikin yanayi irin wannan. Ki sani cewa da sonki nake kwana da shi nake tashi. Ki Huta Lafiya.


Son Ki Ne Linzamin Sarrafa Tunanina

Haɗuwata da ke, wata babbar nasara ce a rayuwata. Son ki a cikin zuciyata ya zamto tamkar wani linzami ne da yake sarrafa tunanina, a saboda haka, da ke nake fatan na rayu har abada. Ina fatan kuma zaki cigaba da raya soyayyata a cikin zuciyarki. Ina Son Ki masoyiya. Wannan sakon safiya ne dake Kara soyayya 


Ina Son Ki Fiye Da Yadda Kike Son Kanki 

An ce kowace kwarya tana da abokin burminta, haka kuwa yake, ni da ke tamkar zara da wata ne, mun dace da juna. Na gode da irin kulawar da kike bani a soyayya, da sannu zan haska ki gane cewa, ina son ki fiye da yadda kike son kanki. Hmm! Masoyiyata, ki kwana lafıya. Sai da safe


Tunanin Κi Νe Αikina Masoyiya 

Shin ko kin san da cewa, a cikin mafi yawancin dare bana iya kwanciya na rintsa saboda tsabar tinaninki? Na kan kwaɗaitu da son ganin ki a koda yaushe, fiye da yadda kike bayyana kullum a cikin mafarkina. Ni ne dai masoyinki, mai fatan kin tashi lafıya. Ki wuni lafıya, farin cikin Raina


Κai Νe Wanda Nake Kauna Masoyi

Shin wai haka ne cewa, SOYAYYA na daga cikin abubuwan da ba a iya gwanancewa a kan su? Matuƙar kuwa haka ne, ni zan yi iya ƙoƙarina wajen ganin na shayar da kai madarar soyayya mai tsananin dadi. Kai ne farin cikin raina, kuma kai ne wanda nake ƙauna, kai ne wanda kuma zan cigaba da so har abada. Ina Son Ka


Ni Na San Na Yi Babban Dace Da Samun Ka Masoyi 

A lokacin da ka kamu da son wani, bai zama lallai shi ma ya so ka ba, amma ni na yi dace da samun wanda ya bani ikon mallakar zuciyarsa cikin taƙama da izza, wanda kuma ya kasance cikin soyayyar zuciyata wato ya kasance nima na kamu da son shi. Kai ne wanda ke kore damuwar zuciyata. Ina son ka sosai abun Alfahari Na


Son Ka Tamkar Hasken Farin Wata Yake A Gare Ni 

Kasantuwar sonka a cikin zuciyata, ya zamto tamkar hasken farin watan da haskensa ke kore duhun duniya. Son ka, ya haske zuciya da saman fuskata, ya haska gangar jiki da saman fatata. Ina Son Ka masoyi 


Son Ka Na Yawo Kullum A Cikin Zuciya Ta 

Masoyina abun alfahira, na kamu da son ka fiye da yadda kake tunani, duk da kasantuwar SO tamkar iska yake da ba a iya gani ko taɓa shi, amma akan iya jin shi a cikin zuciya, tamkar yadda son ka ya kasance cikin sukar zuciyata a dare ko rana. Ina fatan ka yi bacci cikin farin ciki da nishaɗi. Ina Son Ka


Sako Mai Muhimmanci Ga Masoya 

Kana da damar tura wa abokiyar tsinkar furenka, amma ba a amince wani ya yi amfani da shi da niyyar yaudarar wata ruhi ba. Akwai mai ganin Ka/Ki a ko'ina wato Allah. A kiyaye hakkin mallaka, a guje wa satar fasaha.


Waɗannan sune wasu daga cikin saƙonnin Barka da safiya da yake ratsa zukatan masoya. Da fatan kun ji daɗin waɗannan saƙonnin.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post