Dalilin Da Yasa Mata Ke Yin Kuka A Daren Farko |
Dalilin Da Yasa Mata Ke Yin Kuka A Daren Su Na Farko Na Aure
Daren farko dare ne da mata da yawa ke yin kuka da fargarbar abinda zai faru, musamman matan da ba su zubar da budurcinsu a waje ba. Amma budurwa wacce bata san dadin namiji ba idan an yi mata aure a ranar da ta shiga ɗakin mijinta tana shiga damuwa da fargaba tare da yin kuka a daren farko.
Ƴan mata da yawa a satin da za'a yi aurensu suke fara yin kuka don fargabar abinda zai faru dasu a daren su na farko da mijinsu. Wasu suna daina cin abinci ko su daina walwala duk domin tunaninsu kan irin kukan daren farko.
Inaso duk wata budurwa ta sani cewa babu wani kuka a daren farko, ku latsa wannan blue rubutun don Karanta. Yadda ya kamata ango yaiwa amaryarsa a daren su na farko ba tare da ya saka ta kuka ba. Idan namiji yasan matakan da ake bi a daren farko babu wani abin tayar da hankali.
A ƙarshe ina so duk wata mace dake shirin yin aure kada ta tayar da hankalinta kan abubuwan da ake faɗa mata kan yin kuka a daren farko, babu wani abin fargaba. Ki latsa wannan blue rubutun don ki san abubuwan da ake so amarya ta yi a daren farko.