Ciwon Ƙyanda(MEASLES) Da Alamomin Yadda Ake Gane Ciwon

Ciwon Ƙyanda(MEASLES) Da Alamomin Yadda Ake Gane Ciwon
Ciwon Ƙyanda(MEASLES) Da Alamomin Yadda Ake Gane Ciwon 


Ciwon Ƙyanda(MEASLES) Da Alamomin Yadda Ake Gane Ciwon 


Ciwon kyanda ko bakon dauro kamar yadda ake kiransa a zamanin baya, wani ciwo ne da yara da yawa kanyi fama da shi saboda busasshiyar iska ta hunturu da rani da ke kaɗawa a Arewa. Wato su ƙwayoyin cutar iska suke bi sai a shaƙe su idan an yi tari ko atishawa. Wasu kwayoyin cuta na ‘birus’ ne ke kawo ciwon.


Ƙwayoyin cutar sun fi kama yara ’yan kasa da shekaru biyar waɗanda garkuwar jikinsu ba ta yi ƙwari ba. An kiyasta cewa a ɗan tsakanin watannin baya, yara fiye da 2,000 tuni sun riga mu gidan gaskiya a garuruwan Arewa da dama, sakamakon ɓullar ciwon.


Alamomin Yadda Ake Gane Ciwon Ƙyanda

Alamun ciwon ƙyanda su ne da farko yaro zai fara ciwo kamar mura, har idanu su riƙa yin ruwa suna ja, daga nan sai zazzabi, yaro ya kasa cin abinci daga nan sai a ga wasu ƙananan kuraje sun feso masa duk jikin, har baki. Waɗannan kuraje sukan yi ƙaiƙayi sosai. Daga nan kuma ko dai jiki ya yaƙi ƙwayoyin cutar, ko kuma su ci gaba da jawo lahani.


Misali, daga makogwaro har cikin kunne sukan iya shiga su kawo ciwon kunne. A ido ma sukan iya huda farin ido, idan suka shiga kirji kuma su kawo numoniya. Sai an dauki matakin karawa yaro kaifin garkuwar jiki kafin ya iya shawo kansu. Duk wannan yakan dauki misalin sati biyu yaro na fama.


Yara masu karyayyar garkuwar jiki kamar masu ciwon kanjamau da ciwon suga kenan sun fi shan wahala, tun da jikinsu yakan dau lokaci mai dan tsawo yana yakarsu. Amma idan yaro yana da kwarin garkuwar jiki ba za ma a gane kyanda ba ce, domin ’yar mura kawai zai yi ta kwana uku zuwa hudu ya warke. Wasunsu ma ko murar ba sa yi, amma za su iya sa wa wani.


Hanyoyin Kariya Da Magani Daga Cutar Ƙyanda

Hanyoyin kariya daga wannan cuta kan fara tun daga lokacin da aka haifi yaro. Idan aka ba jariri nonon uwa zalla har zuwa lokacin da za'a yaye shi kan iya kare shi daga kamuwa da cutar Ƙyanda. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post