Ƙarin Bayani Akan Cutar Kanjamau (AIDS)

Ƙarin Bayani Akan Cutar Kanjamau (AIDS)

Ƙarin Bayani Akan Cutar Kanjamau (AIDS) 


Ƙarin Bayani Akan Cutar Kanjamau (AIDS) 


Da farko dai Kalmar AIDS na nufin Acquired Immuno Deficiency Syndrome, ma'ana Cuta Mai Karya Garkuwar Jiki da Take Yaɗuwa. Ita kuma kalmar HIV na nufin Human Immuno deficiency Virus (ma'ana Virus Mai Karya Garkuwar Jikin dan Adam). 


Ita AIDS ita ce cutar HIV kuma shine mai jawo cutar ko kuma Virus ɗin. Cutar ƙanjamau na faruwa sakamakon shigar ƙwayar halittar HIV virus, a cikin jikin mutum. 


Hanyoyin Da Ake Kamuwa Da Kanjamau 

1.Tana yaɗuwa ta hanyar jima'i da mai ɗauke da cutar

2.Ta hanyar yin amfani da jinin mai ɗauke da cutar

3.Ta hanyar gurɓatattun kayan aiki kamar reza, wuƙa, almakashi, allura e.t.c

4.Daga uwa mai ɗauke da cutar zuwa ga jaririn dake cikinta ko ta ɓangaren shayarwa 

ƙarin bayani:- akasari kashi 95% na yaɗuwa ne ta hanyar jima'i da mai ɗauke da cutar.


Alamomin Cutar Ƙanjamau HIV AIDS 

Bayyanar alamomin Cutar AIDS ya kan sha ban-ban a tsakanin mutane. Bayan shigar ƙwayar cutar Virus na HIV, alamomi kan iya fara bayyana daga watanni kaɗan har zuwa shekaru goma ko sama da haka. Wannan kuma ya ta’allaƙa da yadda shi Virus ɗin ya haɓaka ya ƙara yawa, da kuma ƙarfin garkuwar jikin mutum da kuma irin yanayin rayuwarshi. Amma dai alamomi na farko-farko sun haɗa da:


• Yawan gajiya

• Zazzaɓi 

• Rama

• Ciwon kaluluwa(lymph nodes enlargement) ko kumburin hamata, kyuiɓi, mara, da kuma maƙwallato (sore throat)

•Zaka ga mutum ya gaza aikin da can yakan yi shi cikin sauƙi.


Bayan haka idan cutar ta ta'azzara, to sauran ƙwayoyin cuta kamar su Bacteria, virus, fungi da kuma parasites and worms zasu samu dama su haɓaka, saboda garkuwar jiki tayi rauni. Ƙarshe cutuka kamar 

1Tarin Fuka

2 Amai da gudawa

3 Kurajen jiki 

4 Kurajen al'aura duk za su bayyana. Akwai dai alamomi barkatai, da zasu iya sha banban daga mutum zuwa mutum.


Yaya Ake Gane Mutum Yana Da HIV AIDS 

Ana iya ganewa ne ta hanyar yin bincike a ɗakin binciken Asibiti  Lab) kuma a tabbatar da hakan daga bakin ƙwararren likita.


Shin Cutar AIDS Na Da Magani 

Maganar gaskiya, har yanzu ba'a samar da shaƙiƙin maganin cutar Kanjamau ba. Sai dai, akwai magunguna masu ƙarfi da suke rage kaifin cutar, kuma su hana ƙwayar Virus haɓaka. Amma dai basu kawarda cutar gaba ɗaya.


Ana Yin Riga Kafin Cutar AIDS Kuwa?

Kamar yadda ake yi wa cutar ƙyanda, sanƙarau, polio riga-kafi, ita Cutar AIDS ba a mata riga-kafi, duk da cewa har yanzu ana kan bincike akan hakan. Amma dai Babban riga-kafi da kuma kariya daga Ƙanjamau sun haɗa da:


1. Barin yin alaƙar jima'i da karuwai, matan banza ko mazan banza

2. Yin awo a asibiti don tabbatar da kuɓuta daga wannan cuta. Musamman ga mutanen da suke da niyyar aure, don kawar da zargi 

3. Tabbatar da tsabtace kayan aikin asibiti kafin a yi aiki dasu akan wani mutum daban

4. Zubar da sirinji da allura a cikin shara tare da ƙone su a cikin wuta

5.Nisantar yawan musayar kayan aiki kamar reza, wuƙar aski, Clipper, almakashin yankan farce, har sai bayan an tsaftace su da wuta ko da Dettol

6. Nisantar duk abinda zai kai mutum aikata zina ko wani abun makamancin haka.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post