Amfanin Yin Jima'i Akai-Akai Ga MACE MAI Ciki |
Yadda Amfanin Yin Jima'i Akai-Akai Ga MACE MAI Ciki Ke Ƙara Musu Lafiyar Jiki Da Jaririnta
Ba kamar yadda wasu ke tunani ba. Jima'i da mace mai ɗauke da juna biyu yana da muhimmanci ga ita mai ciki, cewar masana.
Ga wasu daga cikin amfanin da masana suka kawo su ga macen da ake Jima'i da ita idan tana da ciki.
1:Yakan Sa Haihuwa Cikin Sauƙi
Masana sukace macen da ake yawaita kwanciyar aure da ita bayan ta samu ciki, za ta haihu cikin sauƙi ba tare da doguwar naƙuda ba. Wannan yasa suka baiwa ma'aurata shawaran cewa, kada su sausautawa Jima'i koda kuwa gobe ne macen ake saran zata haihu.
2: Samun Bacci
Jima'i da mace mai ciki yakan sa ta ta samu bacci mai daɗi a duk lokacin da aka sadu da ita. Ana kammala saduwa da mace mai ciki za ta samu wani bacci mai daɗin gaske da za ta manta duniyar da take ciki. Don haka ma'aurata kada su yi kasa a gwaiwa wajen Jima'i da mai ciki.
3: Yana Warware Gajiya
Duk irin gajiya ko damuwa da mace mai ciki take da shi ana saduwa da ita za ta ji wasai inji masana. Wannan yasa duk wata mace mai ciki ya dace a yi Jima'i da ita a lokacin da jikinta ya yi laushi ko kuma ta shiga wata damuwa.
4: Narkar Da Kitse
Masana suka ce duk mace mai ciki da ake yawan saduwa da ita kitsae ba zai taru a jikinta ba. Kowa dai yasan illar da kitsai yake dashi a jikin mutum. Amma ita mace mai ciki ta hanyar Jima'i za ta samu waraka matsalar kitsai a jikinta.
5: Maganin Hawan Jini
Duk wata mace mai ciki akwai yiwuwar ta kamu da cutar hawan jini. Amma idan har tana baiwa mijinta gabanta akai-akai da cikin, ba za ta samu wannan matsalar na hawan jini ba inji masana.
Waɗannan sune wasu daga cikin amfanin yin Jima'i da mace mai juna biyu kamar yadda likitoci suka tabbatar. Sai dai kuma yana da kyau maza su fahimta, akwai wasu matan da kwata-kwata basa son yin Jima'i idan suna da ciki, idan matarka tana cikin irin waɗannan matan, kada ka takura kace dole sai kunyi. Kawai idan tana sha'awar yin Jima'i da ciki to kada ka saurara mata domin samun lafiyanta ne hakan. Idan kuma bata so, sai kayi haƙuri.