Amfanin Shayar Da Yaro Nono Zalla Tsawon Wata 6 - Android Pols

Amfanin Shayar Da Yaro Nono Zalla Tsawon Wata 6 - Android Pols
Amfanin Shayar Da Yaro Nono Zalla Tsawon Wata 6 


Amfanin Shayar Da Yaro Nono Zalla Tsawon Wata 6, Ka so mafi tsoka wajan 87% cikin 100% a cikin Nonon mahaifiya yana ɗauke da ruwa 


Tsarin shayar da Jariri na tsawon wata 6 tsari ne wanda ko shakka babu nufin zaluntar Jariri ko azabtar da shi, sai dai ma bincike ya tabbatar da cewa yunƙuri ne mai kyau wajen tabbatar da ingantacciyar lafiyar Jariri ta fuskar ƙarfafa garkuwar jikin Jaririn, lafiyar tunaninsa, kwarin kashi, kuzari da dai sauransu.


Wasu mutanen sai su ce ya zasu hana Jariri ruwa har tsawon wata Shida? Masu wannan tunanin su sani cewa ba lallai sai ta hanyar shan ruwa irin wanda muke sha bane Jariri zai samu ruwa a jikinsa ba.


Ka so mafi tsoka wajan 87% cikin 100% a cikin Nonon mahaifiya yana ɗauke da ruwa, kunga kenan yaro yana shan ruwa amma sai dai al'umma ba su san da hakan ba.


Abin lura da aka ce a shayar da Jariri zallar Nono shi ne bincike ya tabbatar da jikin yaro ba ya iya fitar da wasu sinadarai, dole sai dai ya iya samun su ta jikin mahaifiya, sannan idan aka yi gangancin bashi wasu abubuwa wanda ba Nono ba, to akwai yiyuwar zai dinga fama da rashin lafiya sakamakon rashin tabbacin tsaftar abinda aka bashi. Ga kuma raunin garkuwar jikin yaro, saɓanin Nono wanda ya ke tahowa kai tsaye daga cikin jikinta zuwa bakin shi ba tare da wani abu a tsakani ba.


Tabbas yara da yawa sun rasu, sakamakon sakaci na rashin amfani da wannan tsari mai matuƙar muhimmanci ga rayuwar jariri da al'umma ba ki ɗaya. Rigakafi dai har kullum ya fi Magani. 


Da fatan Karanta wannan topic zai taimaka muku wajen sanin muhimmanci da amfanin shayar da jariri nonon mahaifiya na tsawon watanni 6. Allah ya datar damu amin. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post